Page 60
Amma a ranar kafin ya tafi haka Haneefa ta sa shi a gaba tana kuka sosai, samun waje wai bata son ya tafi ya barta .Shi kuma ya aje komai ya tsaya ya lallasheta har tayi shiru. Sheik Sadisu kuwa a gaba ya sa shi da cewar, da, da yanzu ba daya bane. Domin da sai bayan watanni biyu yake zuwa ko kuma sai anyi abin zuwa. Yanzu kuma kada ya manta yana da mata wacce a koyaushe take bukatar ganinsa, don haka ya zama dole a yanzu ya dinga kokarin dawowa akan lokaci, saboda iyalinsa. Muhseen ya amsa da cewa. "In sha -Allahu zan yi kokarin dawowa cikin kowane lokaci na samu dama”. Bayan ya sallame da shi, yayi wajen Hajiya Goggo, tana tare da Haneefa tana yi mata sangarta. Ita ma Hajiya Goggon tayi masa yar nasiha. Daga bisani suka yi sallama ya dauki hanyar Kaduna. Cikin natsuwar zuciya da kwanciyar hankali.
Tun komawar Muhseen Kaduna. Sai ya sami kansa tamkar an zare masa kaya ko kuma an sauke masa kaya, domin dai 'yan makonni da yayi tare da Haneefa, a takure yake, a kuma kuntace yake, sai dai babu wanda zai fahimci hakan, kasancewar bai nuna ba. A Kaduna kuwa har mantawa yake yana da mata, don wani lokacin sai Umar ya sako hirarta ko kuma ta kira shi a waya. Sannan yake tunawa da ita. Shi yasa koyaushe ta kira shi a waya, take masa korafin baya kiranta a waya. Sai ka ce bai damu da ita ba. Shi kuma a koyaushe sai ya bata hakuri akan aiki ne yake masa yawa. Amma tana zuciyarsa, don haka idan ta ga bai kirata ba, to yana cikin aiki ne, kada tayi fushi, kada kuma ta ji haushi. A dalilin hakan Haneefa ta yarda da uzirinsa, wani lokacin Muhseen Ya kan koma Jigawa bayan mako daya, ko biyu. Wani lokacin kuma har mako uku yake yi. Ya buge da cewa yana cikin matsanancin aiki ne, don aikin da yake a Kadunan, ba karamin abu bane. Akwai takura da jigata. Ranar wata talata. A ranar kwanan Muhseen daya rabonsa da Jigawa. Haneefa tana kwance a doguwar kujera tana kallon wani (Indian firm), da ake gabatarwa a ta shar (B4U) a dai-dai lokacin Hajiya Sa'a ta shigo falon. Da sauri Haneefa ta tashi tana dariya "Laa! Hajiya"