Page 61
Hajiya Sa'a ta zauna cike da fara'a tace "Autar Hajiya ki na lafiya dai ko na gankl akwance ko hutu ne?" Ta kama dariya tace 'Hajiya hutu ne kawai, lafiyata kalau. Bari na kawo miki lemo". Ta tashi da sauri ta bude frij ta dauko lemon (Five alive), da kofi ta aje a gabanta. Lokaci daya ta na cewa "Ya su Baba? Tace "Lafiya lau, ni ma daga gidan Sameera nake". Haneefa ta koma ta zauna tana cewa "Lafiya dai ko? Yaya Sameeran? “ Ta dan tabe baki, lokaci daya tana kurbar lemon. Sannan tace "Fitina ce ta yau daban, ta gobe daban. Musa yana danne mata hakki, yana kwararta, bata samun komai da shi. Amma Babanku kullum laifinta yake gani. Shi yasa yau nace bari na je na datse shi a gida, ayi wacce za'ayi, domin dai ni ba zan taba yarda 'yata ta sha wahala a gidan auranta ba, ba zan yarda yata ta zama Bora ba." Haneefa tace "To, kin tarar da shi? Tayi kwata tace "Na tarar da shi kuma na yi masa kaca-kaca, na gaya masa ba zan yarda da haka ba, kuma kada ya kara kai kararta wajen mahalfinta, yana hadasu yana sawa yana ganin bakinta." Hannefa tace "Shi yasa nake kaunarki Hajlya, domin kin san yadda za ki kwato ma Ya*yanki 'yancinsu, koda ake ganin fadanki, ai akan gaskiyarki ne." Tayi murmushi tana kalionta tace "Ke ma taka nas na yo miki yau, domin ina ganin tamkar ba ki san inda rayuwa tasa gaba ba, nasa miki ido, na gani ko za ki hankalta. Amma na ga tamkar ki na neman ki manta da abinda yake muhimmi a rayuwarki." Haneefa ta gyara zama tace "Me kuma na yi Hajiya?” Hajiya Sa'a tace "Ba'abinda ki ka yi, sai shashanci da shantakewa da son miji, babu wani ci-gaba." Haneefa tace "Kamar yaya? Ni fa ban fahimceki ba Hajiya". Hailya Sa'a ta dan muskuta, sannan tace tana me dubanta Yanzu da auranki da Muhseen, akalla anyi wata nawa? Haneefa tayi dan shiru alamar tunani, sannan tace "Za'yi watanni shida". Ta gyada kal tace "To tsawon watanni shidan nan, nawa ki ka aje naki na kanki. nawa ki ka banbara a hannun Muhseen?