KALUBALE BOOK 1

Page 62

by @yargidanimam

Haneefa tace "Ba ko kwandala, domin ni tunda muka yi auran nan. Yaya Muhseen bai taba dunkule kudi kamar dubu goma ya ba ni, yace na yi wani abu ba." Hajiya Sa'a ta harareta tace "Yanzu bai taba mallaka miki naira dubu goma ba,haka nan yace ko za ki kashe? “Ta girgiza kai tace "Don dai bukatar kaina, bai taba ba ni ba.Amma yana ba ni, don bukatar gidansa, domin kullum, kuma koyaushe Store din aje kayan abincinsa a cike yake yana matular kokari, domin babu abinda na nema, na rasa. Idan kuma zai tafl yana ba ni dubu goma, ko sha blyar yace ko gida zai bukaci wani abu, baya nan. Yana kolari sosai” Haj Sa'a ta dalla mata harara tace "Kokari, kokarin me? Don yana cikaki da abinci. ai wannan dama dolensa ne, dole ya aje miki abinda za ki ci, kudi kuma da yake baki na hidimar gida ko a cikin ai kya cire na ajiya”.Ta nisa tana kallonta tace "To bari ki ji na gaya miki Haneefa, Idan ki ka tsaya kallon ruwa... ...To kwado zal yi maki kafa, ke kin tsaya tansayin miji idan ke ba ki ci ba, wasu ai sa ci". Haneefa ta dubeta tace "Su waye za sun cin Hajlya? Ta kara harararta tace '"Ke ba ki san masu cin ba? To yan matansa na can Kadunan, ko ki na tunanin yadda yake barinki, yayi mako daya biyu, Uku bai dawo gareki ba, zai rasa 'yan mata ne a can wadan da zasu dinga cin kudinsa, (Wa'iyazubillah! Don Allah iyaye mata ayi hattara. Domin hakika wasunku suna da hannu a wajen mace-macen auran Ya' yansu mata. Haba idan ba ki gyara zaman gidan 'Ya yanki ba, ai bai kamata ki bata ba. Wannan kuskure ne babba. Son abin duniya shi ke hallakar da wasu ¡yayen, don haka ayi hattara). Haneefa me jarabar kishi. Nan da nan ta rude, idanunta suka canja tace "Yanzu Hajlya, Yaya Muhseen din ne keda wasu yan matan? “ Ganin ta shiga damuwa, yasa Haj Sa'a tace 'A'a, ban tabbatar ba, tunanina ne kawai ya ba ni haka Haneefa. Amma ina son ki natsu, ki san abinda ki ke yi. Yakamata ko karya ne, ki dinga yima mijinki, ki na samun kudi. Sai kuma ki dinga kawo min, ina adana miki, ina fatan kin fahimceni? “ Haneefa ta daga kai . Tace "Na fahimta Hajlya." Tayi murmushi tace "To ko ke fa autata". Haneefa dai tunda Hajiya Sa'a ta ambaci Muhseen yana da 'yan mata ta rage walwala, ta kuma rasa natsuwar zuciyarta, fahimtar hakan da Hajiya Sa'a tayi ne, yasa tayi dariya tace 'Autar