KALUBALE BOOK 1

Page 63

by @yargidanimam

Hajiya, sarkin kishi, ke da Allah saki ranki. Muhseen bai da wata budarwa. Haka zalika bai da wata mata da ta wuce ki. Ke kadai ce ba wata" Dariya ta subuce ma Haneefa tace "Allah Hajiya”Tace "Na tabbatar miki da hakan, matukar ina raye". Daga nan Haneefa ta saki ranta. Haka Hajiya Sa'a tayi ta kara tusa ma Haneela ra'ayin banza da wofi, wanda bai kamata ace duk wata uwar kwarai na yi ma 'yarta ba. Da Hajiya ta tashi tafiya har (Store) din Haneefa ta shiga, katuwar leda ta samu ta dibi taliya da Cus-cus da Macaroni da Kwai, tana diba tana fadin "Kin ga shekaran jiya, haka muka wuni ba mu yi girki ba, ni ba ni da kudi. Babanku ko. Kin san ba wani kokarl gare shi ba, jiya ma haka sai karma-karma, shi yasa gara na dan diba, tunda na ga (Store) din naki a cike yake." Haneefa tayi tsaye sototo! Tana kallonta har ta gama dibar abinda za ta diba ta fito. Ta dubeta a sanyaye tace "Ha]iya, amma don Allah kada ki blya gidan Malam, don ba na son Hajiya Goggo ta ganki da wadannan kayan". Ta dubeta a natse tace 'Sai dana gama da wa|en Hajiya, sannan na yo nan, sal dai kuma idan ba kya son dibar da na yi, sai na maida miki? Ta girgiza kai da sauri tace "Haba dai Hajiyata, A'a Wallahi." Tace 'A'to, na gama dai ai ke ce yakamata ace ki na aiko mana da irin wadannan kayan ba tare da mun yi Tsinin keya na tambaya ba, tunda dai kin san koda 'Yan-uwana suke taimaka min, ina cikin bukata, kuma kin fi kowa sanin duk kin Fi 'Yar-uwarki Sameera dacen gidan miji, ba abinda ki ka rasa." Haneefa tayi dan murmushi tace "To Hajiya, na jì, na dauka, zan kuma gyara". Hajlya Sa'a ta kara murmusawa tace "To ni zan tafi". Daga nan Haneefa tayi mata rakiya har kofar get. Sannan ta dawo zuciyarta cike da daukar shawarar mahaifiyarta, domin dai ita ma tana ganin zuwa wannan lokacin yakamata ace Muhseen yayi mata wani kwakkwaran abu, wanda ita ma za ta san tana auran me sukuni. Kusan haka ta wuni cikin tunani da shaukin maganganun mahaifiyarta, wanda take ganin gaskiya ne, dole ta canja tsarin zamanta da Muhseen.