Page 64
A kalla Munseen ya sami kusan makonni uku rabonsa da jigawa kuma bai ma sa ranar zuwa jigawan ba. Ranar laraba yana kwance akam kafet kafarsa daya na kan daya. Fitar Umar kenan daga gidan, Wayar Muhiseen ta shiga kukan neman agajl. Ya tura hannu, ya dauka. Sunan Haneefa ya fito a saman wayar. Da sauri ya dauka, domin baya son tayi masa korafin rashin daukar' wayar da wuri. "Haneefa ki na lafiya? Abinda ya fara fada kenan, tana daga kan kujerar falonta ta amsa "Lafiya lau. Ya aiki? "Aiki ba shi da dadi, tunda yana hanani sakewa da matata." Ta yi murmushi ta jidadin maganarsa, dama ya fada don ta ji dadi ne. Tayi murmushi tace "Ni kaina aikin yana takura min". Yace “ ki kara hakuri, domin ba na son kl yi saurin karaya da aikin nawa, domin kin san aikin , shine rufin asirinmu". Tayi murmushi tace "Haka ne, ni yanzu dalilin kiran wayata, Ina son na gaya maka cewa ina bukatar kudi ne, domin bukatar kaina." Ya dan gyara kwanciyarsa yace "Wace irin bukata gareki Haneefa? Wacce ba za ki iya bari na dawo ba". Ta dan turbune fuska tace "To wa ya san ranar dawowar taka? Ina bukatar dubu goma sha biyar ne, na ankon bikin kawata da za'ayi, kuma gobe da yamma zan bada kudin. Ni kuma ba ni da ko kwandala, kodayake babu bukatar na sanar da kai, tunda ka san ba ni da kudin" Yayil dan Jim! Yace "Yanzu ba'za'a iya hakuri har na dawo ba? "Nace wa ya san ranar dawowarka? Idan kuma yau ko gobe za ka dawo, to ana iya yin hakurin? “ ta karasa magana cikin karfin murya,Ya girgiza kai yace "Ba zan sami damar dawowa gobe ba, gaskiya" "To ni ma ba zan iya hakuri har ka dawo ba, domin hakan zai iya sa na rasa samun ankon, ba kuma na fatan hakan, domin ba zan jure ganin kowa da anko. Ni ba ni da shi ba. Domin ba na son ace ya ga gareni saye ne." Muhseen ya numfasa yace "To shi kenan, ki je ki karba a hannun Hajlyata, zan kirata a waya na gaya mata, ta baki. Yayi ko?" Tayi murmushi "Yayi, nagode sai anjima, don ka kusa cinye min Credit". Daga nan kafin yayi magana ta kashe wayarta, ba tare da ta damu da jin wata maganarsa ba.