KALUBALE BOOK 1

Page 65

by @yargidanimam

Shiru yayi, ya dora wayar a saman kuncinsa. Haneefa bata gajiya da bukatu, komai zan yi mata, domin mu sami zaman lafiya, domin ba ni son aji kanmu. Don duk abinda zai tashi hankalin Malam ko Hajiya, ba na kaunarsa. A zuciyarsa yake fadin hakan, gami da rufe idanunsa ma'abota kyau. Mako daya bayan nan. Muhseen ya je Jigawa. Kwanansa uku, ya dawo Kaduna, bayan ya aje ma Haneefa komai na bukatarta. Ranar wata alhamis. Muhseen ya sami wayar Hajiya Goggo tana sanar da shi Sheik Sadisu ba shi da lafiya. Yana kwance ciwon kirjinsa ya tashi. Nan da nan Muhseen ya gigice, ya shiga matukar damuwa, haka zalika a wannan ranar ya aje komai, ya kwaso hanyar jigawa. Sai cikin dare ya iso sosai, domin a lokacin daya iso gidan karfe goma sha daya da kwata ne, na dare. Kai tsaye gidan Malam ya yada zango, dakin Sheik Sadisu. Hajiya Goggo da Alhaji Sani ke tare da shi, yana kwance idanunsa a runtse, hannayensa biyu a saman kirjinsa, ya dafe. Jin muryar Muhseen ya tilasta masa bude idanunsa. Ya mika hannu yana kokarin riko Muhseen. Shì ma da sauri ya kama shi ya rike. Ya zauna kusa da shi, yana shafa masa kansa a hankali, cikin damuwa yana cewa. "Sannu Malam. Allah ya ba-ka lafiya." Hajiya Goggo ta dube shi tace "Me yasa ba-ka bari sai gobe ba, ka biyo dare haka,duk da ba-ka son tafiyar dare". Ya girgiza kai yace "Ai Hajiya kwanciyar hankalina, shine na ganni a gaban Malam, don haka ko karfe dayan dare aka gaya min lalurar da yake ciki. Karfe dayan zan kamo hanya." HajiyaGogo tace 'Allah ya kara tsarewa, ai jiki ma yayi kyau, don da safe abin gwanin ban tsoro". Muhseen ya dubi Alhaji Sani yace "Baba to me ya hana akai shi asibiti? Ina ganin ai bai kamata a bar shi a gida ba, ana kallonsa." Alhaji Sani yace "Ka san dai kafiya irin ta Malam, kiri- kiri ya ki yarda mu tafi asibiti, ba yadda ba'ayi ba. Amma ya ki*. Muhseen ya kara rike hannunsa, ji yake kamar ya cire civon ya dawo da shi jikinsa, saboda kauna da tausayin Malam, A sanyaye yace "Malam me yasa ka hana akai ka asibiti? Me yasa