KALUBALE BOOK 1

Page 66

by @yargidanimam

don Allah? “ Bai iya cewa komai ba, illa ido daya zuba ma fuskar Muhseen. Daga bisani Muhseen ya bukaci ruwan zam-zam. Dama Sheik Sadisu baya rabo da ruwan zam-zam, don haka nan da nan Haj Goggo ta tashi ta tsiyayo a kofi, ta kawo masa. Muhseen ya amsa ya rike yayi ta addu'o'i yana tofawa. Masu matukar kyau da tasiri. Da kansa ya taso Sheik Sadisu ya ba shi ruwan, ya sha. Ya rage dan kadan, ya bude kirjinsa ya shafa masa, sannan ya aje kofin yana yi masa sannu. Ganin Sheik Sadisu ya dan sami sauki, yasa Alhaji Sani da Hajiya Goggi suka fita. Dai-dai sha biyu da rabi na dare. Muhseen ya matso sosai kusa da Malam. Ya shiga danna masa jikinsa a hankali, cikin matsuwa da damuwa da al'amarinsa, kafin ka ce meye wannan? Sheik yayi barci, barci me nauyi kuwa, wanda tunda ciwon ya tayar masa, bai yi irinsa ba. Muhseen ya dade yana matsa masa jikinsa har zuwa karfe biyu na dare, inda shi ma barcin ya kwashe shi, a kusa da Sheik. Karfe uku na dare Hajiya Goggo ta dawo dakin. Domin ta ga halin da Sheik yake ciki, haka zalika tayi zaton Muhseen ya tafi giudansa. Don ita ma barcin ta dan yi a dakinta, amma tana shiga ta ga Muhseen kwance kusa da Sheik, yana barci. Shi ma Sheik din barci har da minshari. Mutumin da jiya da yau, sai dai ya rufe ido kawai, amma ba barci. Ta dade a tsaye tana kallonsu. Addu'a ta sami kanta da yi na cewar "Allah ya kara jan kwanan Sheik Sadisu. Domin dai so da shakuwar dake tsakaninsa da Muhseen. Duk ranar daya bar duniya, dole Muhseen ya shiga mugun hali.”

Tayi niyyar ta tashe shi ya tafi gidan sa tunda ko ta nan cikin gidan ya na iya bullewa gidansa. Amma sai ta fasa, domin bata son gaba dayansu ta katsé musu barcinsu, wanda yake musu dadi, don haka ta juya ta fita, bata dade da fita ba. Muhseen ya tashi. Agogo ya farà kallo, karfe uku da kwata na dare. Da sauri ya tashi ya shiga bandakin Malam, ya dauro alwalarsa ya dawo ya haye sallayar Malam, ya shiga gabatar da al'adar rayuwarsa, sallar nafilar dare. Yau dai gaba daya addu'arsa akan Sheik ta kare, domin samun lafiyarsa. Sai kuma addu'ar da kullum baya fashin yinta , saboda muhimmancinta a rayuwarsa, wato