KALUBALE BOOK 1

Page 67

by @yargidanimam

Allah ya bayyana masa yarinyar da yake ganin idanunta a cikin mafarkinsa. Kiran sallar asubah ya tashi Sheik Sadisu, jinsa yayi da karfinsa kuma garau, ya juyo yana kallon Muhseen akan sallaya da hannayena biyu a sama. Sha'awar halayyarsa ta kara kama Sheik. Ido kawai yasa masa, yana yi masa addu'a mai kyau a cikin zuciyarsa. Muhseen na shafa addu'ar, ya juyo suka hada ido da Sheik Sadisu. Da sauri ya taso ya zo ya kama shi "Ka tashi, ya kake jin jikin? Ya daga masa hannu yace "Na ji sauki Magajina, na gode. Allah ya saka maka da alheri, domin tabbas addu'arka a gareni, ita ce Allah ya amsa, ya ba ni sauki" Muhseen ya gyada kansa yace "Allah ya kara maka lafiya Malam." Daga nan ya rike shi har bandaki, yayi alwala a daki suka gabatar da jam'i, bayan idarwarsu. Sheik Sadisu ya dubi Muhseen yace "Magajin Malam, ka je ka ga matarka kuwa? Ya girgiza kai yace "Malam ciwonka ya mantar da ni komai, ban je ba, bata ganni ba" Sheik Sadisu ya ci-gaba da kallonsa yace "Kada wani abu ya kara mantar da kai sauke hakkin da yake wuyanka na matarka, na tabbatar ta san ka dawo, ba za ta ji dadi ace har garin nan ya waye bata ganka ba, Muhseen." Yace Na yi kuskure Malam." Ya girgiza kai yace "Na gode da damuwarka a kaina. Allah yayi maka albarka, ya tsareka a kowane mataki na rayuwa" Ya amsa "Amen, na gode." Dai-dai lokacin Hajiya Goggo ta shigo dakin rike da dogon casbaharta. Muhseen ya gaidata, ta amsa cike da farin-ciki ta dubi Sheik ta gaida shi da jiki. Ya amsa da murya me cike da jin sauki. Ita kanta tayi mamaki, don .haka tace 'Malam jiki yayi kyau. Allah ya kara sauki". Ya dubeta cikin so Yace "Na ji sauki sosai, ni kaina ina mamakin karfin da na samu a jikina." '"Dama ai haka abin yake. Duk ciwon da mutum yake, da Zaran Allah ya kawo sauki, sai ka ga tamkar ba mutum ba. Rayuwa kenan, dama ba kullum ake jin dadinta ba." Muhseen ya dubi Sheik yace "Tsoho me ran karfe." Gaba daya suka yi dariya Hajiya