Page 68
Gwaggo ta dubi Muhseen tace "Magajin Malam, gari ya waye, yakamata ka tashi ka shiga wajen Haneefa haka nan. Tunda ya sami sauki" Muhseen ya tashi da sauri yace "Gaskiyarki Hajiya, kun ga tafiyata Malam. Zan dawo na shiryaka, domin tafiya asibiti". Ya wuce. Sheik Sadisu na kokarin ce masa a bar batun asibitin. Yasa hannu ya toshe kunnansa "Ba na jin komai Malam". Ya fita da sauri daga dakin. Sheik Sadisu da Hajiya Goggo na murmushi. Sheik ya dubeta yace "Na yima Allah godiya Maimuna daya ba ni jikan da ya fi tarin yara kaf! Tun daga kan 'Ya'yan dana haifa zuwa dangina, ban ga dan da yake sona ya damu da ni irin Abdul-Muhseen ba. Shi yasa ni kaina yadda nake sonsa, na damu da shi, ban damu da 'Ya'yan cikina ba. Muhseen tun yana dan shekara uku a duniya. Rikonsa da tarbiyarsa ta dawo hannuna, dole na so shi, na kuma damu da lamarinsa". Hajiya Goggo ta dan nisa tace "Batun fadin ka na son Magajin Malam, ai bata lokaci ne, domin kowa ya san hakan. Yaron yana da hanakali ne, dole ya shiga ran duk wanda yayi koda zaman minti ashirin da shi, balle mu da muka tasam ma shekaru arb' in tare da shi. Yana da wata baiwa ta kwarjini da shiga ran jama'a. Fatana dai Allah ya kara tsare shi, ya kuma kawo farin-ciki a rayuwarsa, yadda yake kula damu, kuma Allah ya ba shi wanda zai kula da shi" '"Amen, Maimuna. Ameen".
. Cewar Sheik Sadisu, yana lumshe idanunsa.