KALUBALE BOOK 1

Page 69

by @yargidanimam

Muhseen yayi sallama, tafi biyu, amma ba a amsa ba, tamkar ba kowa a gidan. Yayi zaton ko Haneefa bata tashi barci bane, duk da a lokacin takwas ta kusa na safe, don haka kai tsaye dakinta ya shiga, tana zaune kan sallayarta. Ta jingina da jikin bango, da alamar tunda ta idar da sallar asubah bata tashi ba, Ido kawai ta daga ta dube shi. Ta kauda kai , ba tare da ta ce masa uffan ba. Bakin gado ya zauna cike da murmushi yace "Idan addu'a ake, a saka da mu." Nan ma bata tanka masa ba, illa ma mikewa da tayi, ta aje hijabin- ta, ta juya za ta fita, Da sauri yasa hannu ya janyo hannunta, ta fado jikinsa. Yasa hannu ya rungumeta. Har kullum kokari yake ya nuna ma Haneeta yana sonta, kullum boye gaskiyar zuciyarsa yake. Nan da nan Haneefa ta shiga turje-turje, yasa bakinsa kusa da kunnanta yana magana a hankali "Haka macen kwarai take tarbar mijinta Haneefa? Ta dan harare shi. Duk da baya gani, domin fuskarta a juye take, tace cikin katuwar murya ba kissa ba, lya kisisinar mallakar miji , sai cewa tayi “Ai mijin kwarai ake ma kyakkyawar tarba", Nan da nan Muhseen ya Ji zuclyarsa ta raunana, domin kullum burinsa bai wuce ya zama mijin kwarai ba, bai wuce ace yana kulawa da matarsa kamar yadda addininsa ya tanadar masa. Ya dan sassauta rikon da yayi mata, wanda yasa ta zare jIkinta, ta tashi tana yi masa wan sakaran kallo. A hankall yace "Haneefa ashe ni ba mijin kwarai bane a gareki? Ta kara fadada murya. Abinda ba'a bukatar duk wata macen kirkl tayi ma mijinta, domin sassauta murya da tausata salon magana suna taimaka wa wajen kara ma namiji son Matarsa tare da ganin darajarta. Amma banda su Haneefa, wacce gaba daya ma na fuskanci bata san salon zama da miji ba, koyin mahaifiyarta ta ke bi .domin fadada murya tayi da karfi. Tace "Da kana tsammaninka a cikin mazajen kwarai ne? To ka y kuskure, domin ba-ka san darajata ba, ba-ka kuma damu da ni ba, tunda har ka lya dawowa tun sha dayan dare, amma ba-ka damu da ka 2o ka ganni ba, ka yi zamanka a cikin gida, ni a