KALUBALE BOOK 1

Page 70

by @yargidanimam

haukata ai na dauka komai runtsi, nice za ka fara gani, kafin kowa, Amma ba-ka damu da haka ba, kana can karewa ma can ka kwana," Cikin rashin jin dadin maganganunta da gajiya da ihun da take masa ya dubeta yace 'Ita kenan matsalar? To ki yi hakuri, nayi kuskure" Matsalar mace kenan da zaran tana fada, ta ji irin wannan furucin daga mijinta, maimakon ta saduda, ta kuma ji dadi, har ita ma ta ba shi hakuri. A'a, maimakon hakan, sai ka ga ta kara rikicewa da fada da masifa, salinka ce mara kan gado. Hakan ce kuma ta kasance ga Haneefa, domin kawai sai ta kara bude murya tana ci- gaba da fadan magana mara dadi. A dalilin hakan Muhseen ya tashi tsam! Ya bar dakin, cikin bacin ran da baya misaltuwa, don baya son ya biye mata, shi ma ya zama Irinta. Yana fita. Dakinsa ya nufa, yayi wanka, ya kintsa kansa. Ya fito, ya bar gidan wanda har zuwa lokacin Haneefa na cikin dakinta. Muhseen tafe yake zuwa gidan Malam, yana tunanin yadda zai yi da hali irin na Haneefa . Mata ce, tamkar ba tayi karatu ba, bata san yadda za ta zauna da mijinta cikin arziki ba. Nan kuma wai tana ikirarin tana kaunarsa, wanda ko kake kauna, ai ba za ka so bacin ransa ba, domin ko shi da baya jin wani shahararran sonta a zuciyarsa, baya kaunar bacin ranta. Amma Haneefa bata da hakuri, ko yaya jefo maganarta take, bab tare da tayi la'akari da za ta yi maka dadi, ko ba za ta yi maka ba, duk zuwan duniya da zai yi, sai sun sami sabani. Abinda baya kauna kenan. Yana bukatar ya rike Haneefa cikin mutunci da kulawa, saboda kakanninsa masu kaunar auran nasu. Yana shiga gidan Sheik. Dakin Hajiya Goggo ya shige. Baifi minti daya da zaunawa ba. Hajiya Goggo ta shigo dakin tana kallonsa "Ka dawo? “Ya gyada kai yana kokarin boye damuwarsa 'Na dawo Hajiya, taimaka min da abin karyawa." Ta dan tsare shi da ido tace 'Matarka fa? “ Ya dan dubeta da kyawawan idanunsa yace "Bata gama ba, ni kuma ba zan iya jira ba, don rabona da abinci tun ranar jiya." Hajiya Goggo ta tashi da sauri ta fita. Zuwa can ta dawo da tiren kayan karyawa, da kanta ta hada masa komai, ya ci, ya koshi Hajlya Goggo tana ganin, damuwa a fuskarsa, sai dai ta fahimci bai