Page 71
son ta gane damuwar tasa, don haka yasa bata tambaye shi komai ba, sai ma hira da ta dinga jansa da ita. Inda ta dube shi tace "wai kos din da kake a Kadunan, har yanzu bai kare ba? Ya dubeta yace "Kin kosa na kara nisa dake ne? Ta girgiza Kai tace "A'a, ni na so haka, fargabar hakan ne ma ya sani yi maka tambayar". Ya kwantar da jikinsa a saman kujera sasai, yace "Shekara biyu ne Hajiya, akalla yanzu saura watanni blyu mu kammala. na tattara na koma asalin wajen aiki na, na kara yin nisa da ku sosai ." Haj Gwaggo ta nisa tace "Allah dai ya kara taimakawa. Allah ya kara daukaka wa|en alkin nan naka". Yace "Amen", Ya duba agogo, sha daya "Yakamata ace yanzu muna asibiti, bari ki gani”Ya yunkura ya tashi. Tare suka Fito Da Haj Gwaggo har dakin Sheik Sadisu. Ya kasa yi ma muhseen musu duk da baya son zuwa asibitin Muhseen da kansa ya shirya shi, ya riko shi har cikin meta, Daga nan sai asibiti, Zuwansu asibitin, ba'a dau wan dogon lokaci ba, aka fara duba Sheik Sadisa, Hakika cutar gembon ciki (Ulcer) tayi masa yawa a ciki, Ita kuma ke haddasa masa tsananin ciwon kirji. Me kamar ana hura masa wuta, Sheik ya dade da ciwon, domin tun kafin halhuwar Muhseen ya sami wannan mummunan ciwon. Likitan yayi masa kyakkyawan duba, ya kuma rubuta Masa magunguna masu kyau wadanda dama ya riga ya saba shansu. Daga karshe suka dungumo suka dawo gida. Sai bayan sallar la'asar. Sannan Muhseen ya koma gida. Haneefa na kwance tana sana'ar, wato kallon fim, da abinda yake kararta da shi, A ciki ta amsa masa sallamar. Ya tsaya a kanta yace "Haneefa make damunki ne har yanzu ba ki shiga kin duba Jikin Malam ba? Ta dago ta dube shi tace. "Na ga wai ka na can ne, Idan na je sai abin yayi yawa” Muhseen ya numfasa rai baco yace "Wace irin magana ce Wannan Kl ke yi mara kan gado idan ina wajensa, sai ki kasa zuwa ki duba shi. Saboda ba Ki da hankali?” Tace a fusace "Da hankalina garau! Ba kuma fadan da za ka yi min, domin dai duk matsayinmu daya a wajen Malam din, duk jikokinsa,.ne mu, sai dai bambanci daya ya fi son ka”
Ku dakace ni
Daga taskar
Yar gidan Imam KALUBALE BOOK 1 DAGA HABIBA ABUBAKAR IMAM (MRS ALIYU MAYERE)
Bismillahir Rahma Nirrahim