Page 72
"Ban nemi wata doguwar magana ba,balle ki cigaba da tsaida kafaffun idanunki a kaina, ki tashi ki je, ki duba shi yanzu, domin ina son ki sani ko da kike tunanin ke ma jikarsa ce, na rantse miki akan ki taba mallam ko ki nuna shi din ba kowa ba ne , zansa fuskar da baki taba sani na da ita ba na ladaftar da ke." Daga nan bai saurari kunkuni da korafin da take ba, ya wuce ya bata waje. Zaunawa yayi a dakinsa, yayi tagumi. Haushin maganar Haneeta na bata masa rai kwarai da gaske rashin shiga ta duba mallam ya taba masa zuciya,neman fitina kawai take da shi, ba ko zai biye mata ba domin damuwar ciwon mallam shi ne a gabansa, yana jinta, sai da ta gama kallonta, ta kara bata lokaci. Sannan ta fita gaida Sheik Sadisu. A can din ma bata dadè ba, bayan ta duba shi, ta shiga wajen Alhaji Sani ta gaisa da matansa, sannan ta dawo dakin Hajiya Goggo, nan ma 'yar hira suka taba, sannan tayi sallama da ita, ta dawo gida ta tadda Muhseen kwance kan doguwar kujera, yana kallon tashar (A.I.T). A fusace ta shigo, sai ka ce wacce aka wurgo, ba sallama. Ido ya daga ya dubeta, ya girgiza kai yace "Kin dawo?" A ciki tace "Uhm." Gami da wucewa fuuu! A hankali ya kira sunanta 'Haneefa zo nan". Ta dan yi jim! Kafin ta tako ta dawo ta zauna, ba tare da tace uffan ba. Ya tashi ya zauna yana kallonta a cikin damuwa, yace "Haneefa wai meke damunki ne?" Galala tayi tana kallonsa tace "Ban fahimceka ba? Ya nisa yace "Ba na jin dadin yadda ki ke tafiyar da ni, menene haka? Me na yi miki da zafi? A fusace ta dago da kai za ta yi masa hayagaga, yayi saurin daga mata hannu. Yace "Don Allah ki yi hakuri, ba na bukatar jin komai daga gareki, in dai don ni ne, to don Allah ki yi hakuri, ki daina min irin wadannan abubuwan. Aure muke, ba wasan yara ba. Yakamata na samu martaba daga gareki, a matsayina na mijiki, kin san zunubin da ki ke dibar ma kanki kuwa? Haneefa ko meye, ba ki iya hakuri". Haneefa tayi shiru tana jinsa, anyi sa'a har ya gama bata yi magana ba. Kuma da gama fadin maganarsa ta kusa minti blyar, ba tayi magana ba, daga karshe tace "To, shi kenan, komai ya wuce". Ta tashi ta fada kicin ta shiga hada-hadar girki. Wanda da bata yi niyya ba. Cikin dabi’ar muhseen ce bai iya fada ba kuma baya son fada, sannan duk inda ya fahimci a dalilinsa wani na fushi bai samun nutsuwa har sai ya ga farinciki a fuskar mutumin.Tsawon kwanaki uku. Muhseen na bi da Haneefa yadda take so. A dalilin baya kaunar su samu katuwar baraka. Sheik Sadisu yayi garau! Don haka Mahseen yayi nufin komawa Kaduna. A daren ranar da zai tafi, yana sanye cikin riga da wando masu santsi na barci, ya wuce Haneefa a falo. Ya nufi (Store).