Page 73
Domin ya duba ya ga ko akwai abinda ya kare, wanda yake ganin mawuyaci ne ma ya ga wani abun ya kare, domin ya wadata (Store) dinsa da kayan abinci. Amma wani abin mamaki (Store) din nasa muna lya kiransa karkaf! Domin mafi yawanci babu komai cikin Kwalayen taliya da Macaroni da su Cus-cus, duk ba komai. Ya dudduba ko'ina, ya koma ya tsaya sototo! Cikin matsanancin mamaki. Daga bisani ya kwala ma Haneefa kira. Ta dan bata lokaci kafin ta shigo (Store) din, "Ya aka yi ne Babban Yaya?” Ta fada ,Ya juyo yana kallonta yace "Mamaki nake yadda na cika (Store) din nan, kafin waccan tafiyar tawa, amma na ga ba komai a ciki, kusan komai ya kare."ta gyara tsaiwarta cike da masifa tace "Shine ka kirani, ka tambayeni?” Tayi masa tambayar a gatse yace cikin karin mamaki '"To ai ke yakamata a fara tambaya, cikinki ke kadai. Amma ace abinci har ya kare? Nan da nan ta hade fuska tace "To me kake nufi? a takaice dai ka na nufin ina yi maka satar abincin ina sayarwa, ko kuma Ina alka ma da talakawan mahalfana...? Ya katseta da sauri yace 'Kada kl juya min maganata, haka nace miki? Me yasa ba ki da fahimta ne? Tace 'Saboda ba-ka koya min yadda zan fahimtan ba". Muhseen ya juya da sauri cikin kufula, ya fita daga (Store) din zuwa dakinsa, yana kokarin mallakar fushinsa domin ba ya son su yi rabuwar tsiya da ita.A wannan daran dai ba’ayi wani harkar arziki ba tsakanin babban yaya da matarsa ba.domin bata kawo kanta ba shi ma kuma bai nemeta ba. Washe gari da wurl ya shirya barin Jigawa. Yana zaune tare da Haneefa ya danne komai , bai kara taso maganar kayan abinci ba. Ya mika mata dubu ashirin yace "Ga shi nan ki dan sayi abinda babu, domin ban yi zaton zan tadda kayan abincin sun kare ba, ba ni da wadatattun kudi, ki yi maneji da wannan kafin na dawo." Ta amsa ta'aje kan kujera, ba tare da tayi godiya ba kamar yadda matan kwarai su ke yi.sannan ta dube shi tace "Sai dubu hamsin da nake son na sayi injin saka, don ba na son na manta yadda ake yi, tunda tuni na koya, na kuma lya, zaman kuma ya dament, ba abin yl." Muhseen ya dubeta yana mamakin yawan bukata Irin ta Haneefa. Kullum ya dawo, salinya tadda bukatarta, wanda idan bai yi mata ba, babu zaman lafiya. Ya cl-gaba da kalionta, sannan yace "To na ji amma ki yi hakuri har sai na kara dawowa". "Saboda me?" Ta fada a turbune