Page 74
yace 'Saboda a yanzu na gaya miki ba ni da kudi, banda isassun kudi, don a jikina yanzu gaba da baya dubu takwas ya rage min, kuma ko can ba ni da kudin, sai na shiga banki, ayi hakuri, ayi min uzuri". Tace a hankali "To shi kenan, idan dai ka ga za ka dade ba. ka dawo ba, ni kawai ka aiko min da su". Bata damu da dawowarsa ba, sai kudin da zai bata, kallonta kawai yayi yace "To shi kenan" Daga nan ya tashi yayi sallama da ita, ya fita ko rakiya bai samu ba. Can ma gidan Sheik bai zauna ba. Sallama yayi da su, ya kwashi hanya domin duk ya kosa ya bar Jigawa. Don Haneefar tasa, ta dura masa zafi, haushinta yake ji. Karfe tara da kwata na dare a falon Muhseen, daga shi sai Umar. Umar ya gyara zamansa yace "Muhseen ina ganin damuwa a tare da Kai, tun tsawon kwanaki biyar da dawowarka daga Jigawa, ko ciwon Malam ne ke taba-ka? Muhseen ya dago, ya dube shi, ya girgiza kai. "A'a Umar, jikin Malam ba matsala, amma ina da tambaya da nake son na yi maka". "Ina jinka". Cewar Umar Muhseen yace "Kowane mutum ne yake samun matsalar zaman aure da matarsa? Me kuma ke haddasa samuwar matsalar? Umar ya tsare shi da ido yace "Ba kowa ne ke samun matsalar zaman aure ba Muhseen, kuma rashin fahimtar juna ke kawo matsalar aure". Muhseen ya numfasa yace 'Umar ina fuskantar matsala daga Haneefa, duk son da take ikirarin tana yi min. Haneefa bata barin zuciyata sukuni, ina iya kokarina wajen nuna mata kauna da kulawa, amma kullum tana nuna min ba na yi mata komai, ban damu da ita ba, ni ba mijin kwarai bane. Idan ka ga yadda Haneefa take yi min Magana, sai ka dauka da yaro dan yaye take. Ta rainani, rainin da ban taba zaton za ta vi min irinsa ba" Ya matso kusa da Umar yana kalionsa, a dame, yace 'Ka fi kowa sanin halin da nake ciki na rashin son mata. Amma na takurama kaina. Dole sai na so Haneefa saboda ina kwadayin mu zauna lafiya, ina son na sauke hakkin dake wuyana nata, ba na son Allah ya kamani da laifin kasa kulawa da hakkinta.