Page 75
Haka zalika Ina kwadayin na faranta ma Malam da Hajlya rai , ta hanyar riketa cikin amana, Amma Haneefa halinta daban yoke Umar. Kuma halinta ya isheni, abin na damuna kwarai da gaske". Umar ya numfasa shi ma cike da damuwa yace "Muhseen ka na nufin ka ce tun auranka da Haneofa a haka kuke? Ya gyada kal "Tsawon auen mu a haka Haneefa take a guna. Da dai bata damu da yawan tambayata kudi ko dora min lalurar da tafi karfina ba. Amma daga baya sai ta tsiri haka. Amma batun tsiwa da raini wannan tun kafin mu cika mako daya da aure ta fara yi min. Amma ina danne damuwata.
Umar yay tsakin Jin haushi yace "Amma ban taba tsammanin haka daga Haneefa ba, yarinyar da nake yi mata kallon me hankali, kuma me kaunarka. Me yasa haka? Kai da nake tunanin za ka kawo matsala, sai ga shi ka na taftyar da al'amuranka gwanin ban sha'awa, amma Haneefa ta bata rawarta da tsalle. Amma Ina me kara ba-ka shawara akan ka yi hakuri, ka kara hakuri, illiminka ya ci-gaba da yi maka rana da amfani. Kada ka bari wata baraka ta bullo daga gareka. Ka ci-gaba da fahimtar da ita illar rayuwar da ta daukar ma kanta, kada ka manta auran zumunta yana da matsala. Kuskure kadan,komai na lya cakudewa, ka fi kowa sanin halin da ake ciki, a yanzu kowa kansa yake so. Don haka dole sal ka yi taka tsan-tsan! Muhseen ya numfasa gami da lumshe ido yace "Na gode da shawararka, dama hakuri kullum a cikinsa nake, ka san ba abinda ya fil burgeni a rayuwa irin hakuri." Umar yace "Ni ma na san haka. Allah yayi mana jagora." Daga nan suka ci-gaba da tattaunawa. Tun dawowarsa, kullum sai ya sami wayar Haneefa tana yi masa tuni da korafin duhu hamsin. Dan dole sai da ya ara wajen Umar ya alka mata da shi. Tun daga ko ranar da Kudin suka iso hannunta, bata kara kiransa a waya ba, don washegarin ranar daya aika mata da kudin, Ta shirya ta tafi gidansu, tayi sa'a, domin Haj Sa'a shirin fita take.