KALUBALE BOOK 1

Page 76

by @yargidanimam

Sai ga ta, nan da nan maganar fita ta fasu, domin dai a yanzu ne Haneefa take autar Hajiya, saboda so da kaunar da take nuna mata, a dalilin cikata da abin duniya da take yi. Hajiya Sa'a ta dubeta cikin murmushi tace "Na yi zaton zan ganki da dan kunshi". "Na me?" "Na abinci, tunda na ga kwana biyu shiru." Ta nisa tace 'Ai Hajiya (Store) din nawa ba komai, don wannan zuwan bai sayi komai ba, ya dai ba ni dubu ashirin, wai na dinga saye, kafin ya dawo. Sai korafi yake kayan abincin sun kare da wuri. Me na yi da su? Cikina ni kadai, ka za-ka za, sai kumfar baki yake”, Hajiya Sa'a ta saki tsaki tace "Dama yadda yake nan, wanda magana ke masa tsada ashe fada gare shi? " tace “Ai ko fada gare shi Hajiya." Tace 'Da Allah fita batunsa, inda ace shi dan mutunci ne, yadda yake ma mahaifiyarsa Hajiya Hadeeza, ai haka zai dinga yi min, yadda yake hidima da ita, haka yakamata ya dinga min, amma sai yayi zuwa hudu, da kyar zai leko sau daya mu gaisa. Ya tashi kuma ya kakkabe rigarsa ya tafi, ko taro baya aje min. Ai ni yadda na yi tsammani, ba haka bane, don na yi zaton zai dinga yi min ruwan kudi, tunda yana auran 'yata." Ta dago tana kallonta tace "Amma tun auranku, ban daura zanin Muhseen sau biyu ba; Haba jama'a." Haneefa ta tabe baki ita ma tace "Ai shi babu ruwansa Hajiya, bai damu da ya san bukatunku ba, ni kaina ban san tunaninsa ba, kin ga wancan dawowar tasa, ba ki ga atamfofi da lesissikan daya ba ni na kai ma mahaifiyarsa ba". Ta dan harareta tace "Ke kuma ki ka kai? Ba ki tuna masa ke ma ki na da mahaifiyar, ba tunda shi ya manta. " Tace "Ni haushi ma bai bari na yi magana ba." "Ita kuma Hajiya Hadeezan bata tambayeki ya aiko min da nawa ko bai aiko min da shi ba." Tace "Bata ce komai ba, Hajiya ko godiyar kirki ba tayi ba, sai dai ya sha sa albarka'. Hajiya Sa'a ta saki tsaki tace "Ba komai, na kusa yin maganin abin." Tace "Me za ki yi Hajiya?" Tace 'Sai lokacin yin yayi, sannan zan gaya miki kome zan yi, kada kuma ki kara tambayata". Ta rufe bakinta da hannu tace "Ba zan kara ba," Tayi dan murmushi