Page 77
tace tana me rikota "Autata, autar mata farar haihuva, ni ai yanzu ke ce gatana, komai zan kulla, sai na yi shawara dake Haneefata". Haneefa ta ji dadin maganarta, ta janyo jakarta ta fito da Naira dubu hamsin. Ta cire dubu goma ta mika ma Hajiya Sa'a dubu arba"in. Ta amsa da sauri cike da fara'a tana kallonta "Na meye Haneefa? Tace "Duhu hamsin na amsa a hannunsa nace zan sayi injin saka." Hajiya Sa'a ta gyara zama cike da jin dadi. Tace "Yauwa Haneefa, haka ake so, ai ma kin amshi kadan da kin ce masa irin dan dubo darin nan ki ke so. Tunda ai yana da kudin, kuma ko yanzu haka za ki gaya masa ki ce kin tambaya, an gaya miki cewa na dubu hamsin din ba shi da kyau, gara na dubu dari." Shigowar Malam Jibrin kenan, ya riski maganar tasu. Haneefa tayi murmushi tace "Haka za'ayi Hajiya, zan kara amso dubu hamsin din, tunda ta bakinki ne, akwai kudin. Amma koyaushe sai ya dinga kokarin nuna min ba shi da kudi, bayan na san yana da kudin". Ta tabe baki tace "Gara da ki ka san hakan Haneefa, kuma ko kadan kada ki ce za ki dinga tausaya masa. Da zaran kin ga ya dan sami kudi masu kauri, ki yi kokari ki ga kin sami koda rabi ne, don Idan ki ka ce za ki tsaya tausayin miji, sal ki kai kanki ki baro, don shi ba zai tausaya miki ba" Malam Jibrin ya kasa jurewa da munanan furacin dake fita daga balin matarsa. A gaggauce ya dage labulen dakin, ya shiga, wanda hakan yayi sanadiyyar katsewar hirar tasu. Haneefa ta dube shi cike da fara'a, tace "Sannu da dawowa Baba, mun sameku lafiya? “ Ya sakar mata harara, yace 'Ban sani ba. Haneefa Ina yi miki kalion me hankali, kin san abinda ki ke yi. Ashe ba haka bane, ke ma kin bi hudubar banza, ta mahalfiyarki, to ina tabbatar miki da cewa za ki tafka kuskure a rayuwarki, domin babu abinda ya fi miki mutunci da daraja, Irin auranki da kuma daraja mijinki." Hajlya Sa'a ta dube shi a kufule tace 'Wace Irin huduba nake mata? Ni dai har abada ba zan yi gwaninta a wajenka ba, menene kuma, kai ba-ka san maganar da muke ba,kawai ka ara, kayafa"