KALUBALE BOOK 1

Page 78

by @yargidanimam

Ya dubeta yace "Na dade tsaye, na kuma fahimci maganarku Gaba daya, kada ta ji tausayin mijinta, ko saboda ke ma ba kya tausaya min, to bari ki ji Haneefa, duk matar da bata tausayin mijinta, bata a cikim jerin mata salihai, Ki ji tsoron Allah, ki rabu da maganganu da rudin banza, na mahaiflyarki". Ya dubi Hajiya Sa'a rai bace. Yace "Da Haneefa da Muhseen. Idan ki na da hankali, duk dai ya'ya ne a wajenki, bai kamata ki banbantasu ba, kuma ko ba "yarki. Muhseen ya aura ba, to ke me iya tsayawa tsayin daka ce ki ga ya, sami kwanciyar hankali a gidansa, Amma na rasa irinki, na kuma rasa irin tunaninki a rayuwa." Ta dube shi fuska turbune tace "To ni dai don Allah ya isa haka, don ban ga abin hayagaga ba". Malam Jibrin ya maida kallonsa ga Haneefa yace "'Me ki ka zo yi? “ A hankali tace "Na zo na gaidaku ne". a fusace yace “To mun gode, maza tashi ki koma dakin mijinki, maza-maza, kuma ba na son na kara ganinki a gidan nan ba tare da kwakkwaran dalili ba, gaisuwar ta isa haka. Tashi ki kama hanya". Hajiya Sa'a tace "Na ji ikon Allah. Yau na ji inda za'a hana "ya zuwa duba uwarta. Ai ko Wallahi da sake". "To ki yi abinda za ki yi, duk talauci na dai, gida dai nawa ne, don haka nace kada na kara ganinta a cikinsa, ba tare da wani dalili mai karfi ba". Suduf-suduf! Haneefa ta tashi ta yafa gyalenta , ya dubeta yace "Yanzu ki na matsayin matar aure, amma ki ke yafa wannan dan gyalen da ba shi da maraba da abin tatar koko, ki yi hankali Haneefa. Duniya ce." Ba tace komai ba, ta karasa yafa gyalen , ta dubi Hajiya Sa'a tace "Hajiya, na tafi." Ba tace uffan ba, saboda haushi har ta fice, ta bar gidan. Malam Jibrin ya dubeta ya saki tsaki, ya juya ya fita cikin fushi, ta hau fada "Ka gama abinka, kai keda aiki, don babu abinda za'a fasa, sai dai ka yi ta sa idonska, sana'ar banza". Duk da yana jinta, bai tanka mata ba, don a kullum Hajiya Sa'a tamkar karamar yarinya take, gaba daya bata da hankali balle lissafi, sai ka ce mara ilimi. Washegari Hajiya Sa’a na shirin fita zuwa inda za ta, jiya bata sami damar zuwa ba a dalilin zuwan Haneefa Sameera. Ta fado gidan gyale a hannu tana tsinka ihu, tamkar wacce aka gaya mata