Page 79
sakon rasuwar danginta duka. A gaggauce Hajiya Sa'a ta tareta cikin tashin hankali "Sameera menene me ya faru na ganki haka?” Cikin kuka Sameera ta juyo fuskarta ga Hajiya Sa' a tace "Hajiya, ni da Musa ne, dubi fuskata, duka na yayi tayi, sai ka ce ya sami jaka. Da kyar makwabta suka kwaceni a hannunsa". Hajiya Sa'a ta daki kirji, gami da fiddo idanu waje tace '"Musan ne yayi miki wannan aikin? Na rantse ba zan yarda ba". Ta karasa sa gyalenta ta janyo hannun Samera, suka fice kai tsaye sai gidan Musa. Sun tadda zai hau mashin dinsa kenan, dake kafe a kofar gida "Dakata, tsohon macuci, tsohon azzalumi, to ba Jaka na haifa maka ba. Musa ba-ka isa ba, da za ka nemi hallaka min ya da bugu ba, don takamar kana auranta. Me tayi maka?”. Musa ya tsaida kallonsa akan Hajiya Sal'a cikin bacin rai yake sosai, yace "Hajiya kada ki nemi tara min jana’a akan gaskiyata . 'Yarki ce na gaji, tunda a kullum goyon bayanta ki ke, gani ki ke kamar ni' ke zaluntarta, ki na zuwa ki na kulla mata maganar banza a kaina. Talauci ai ba kaina farau ba, don kawai ina talaka, sai na zauna gidana ya fi karfina. To na gaji." Ta zakalkalo masa "Eh, ka yi ta gajiya, ita ma ta gaji, ai auran babu dole, banda zaman wahalar da take, me kake tsinana mata? Ba omo, ba sabulun wanka. An gaya maka baiwarka ce? Mugu kawai, azzalumi, dama Sameera ai ba tsarar auranka bace. Allah ne kawai ya kaddara mata, don ta haihu daya da kai, sai aka gaya maka ba za ta iya rabuwa da kai ba". Musa yace "Ni kuma sai aka gaya miki idan na rabu da ita, zan rasa matar aure? To kafin ta cika iddarta, idan na ga dama zan iya aje mata hudu." Hajiya Sa'a tayl shewa tace "Da wane kudin za ka auri mata hudun? Ko daya, yanzu sai an taimaka maka, tunda na ga alamar kai ne ka yanke ma talauci cibiya". Ya buga mashin dinsa ya bula musu hayaki yace "Kanku ake ji". Ya figi mashin dinsa ya bar wajen, daga nan Hajiya Sa'a ta cl-gaba da zuba sababi da masifa har gida. À kofar gida ta tadda Malam Jibrin yana shimfida tabarma, domin matasan dake zuwa daukar karatu. Ido ya tsaya yasa ma Haj Sa'a da 'yarta Sameera har suka shige cikim gidan. Ya numfasa cike da bacin rai, ya wuce shima ya bi