KALUBALE BOOK 1

Page 80

by @yargidanimam

bayansu, ya tadda Hajiya Sa'a na lallashin Sameera "Ki daina kuka, auranki da Musa sai dai idan ana yi a lahira, amma a duniya dai an bar shl, an daina, ba kuma za a kara yayinsa ba." "Cewar wa?" Inji Malam Jibrin, ta juyo a fusace tace "Cewa na." Yace "To ai da sauki, tunda ba cewar Allah bane, idan kuma zamanta da Musa bai kare ba, babu wanda ya isa ya karar da shi". Ya dubi sameera cikin bacin rai yace "Me ya hadaki da mijinki?”, Bai karasa Magana ba, wani yaro yayi sallama. Ya tsagaita da maganar yana kallonsa, '"Wal ana sallama da kai, in iji Musa". Da sauri Malam Jibrin ya juya ya fita waje. Zaune ya tadda Musa a saman tabarma, shi ma ya sami waje ya zauna, a ladabce ya gaida shi, ya amsa cikin kaguwa yace "Musa me ya faru tsakaninka da matarka? Duk hakurinka da juriyarka dana sanka da ita?”. Musa yayi kasa da kansa cikin ladabi yace "Malam don Allah ka yi hakuri, amma ina ganin zamana da Sameera ba zai yuwu ba, dama darajarka take sawa nake raga mata a duk abubuwan da take yi min. Malam Sameera ta riga ta rainani, ba zan taba jin dadin zama da ita ba." Malam Jibrin yace "Ka kwantar da hankalinka Musa, ka yi min bayanin komai da abinda ya hadaku", Musa yace 'Malam ni talaka ne, ba ni da wani karfi , don haka ban ga dalilin da zai sa Sameera ta dinga dora min bukatarta wacce ta fi karfina ba, na san ba na jin dadin zama da ita, bata mutuntani, ina daurewa. Motsi kadan ta kira min talauci, don yanzu ma abinda ya hadamu, akan nama ne, wai ita ta gaji, ta dade bata sa nama a bakinta ba, kullum sai dai ta sha miya lami. Na jera kwana biyu, ina hado cefanen girki, amma bata girkawa, tace in dai bada nama na hado ba, ba za ta girka komai ba. Sai dai na yi ta yin asarar kayan girkin. Shine na gaji yau, dana kawo, ta ki girkawa. Ni kuma ba ni da halin sayo naman, shine na yi mata maganar cewa ba zan yarda da wannan wulakancin ba. Shi kenan Malam Sameera ta rufe idonta, tayi ta gaya min maganganu marasa dadi, har da zagi. Wanda haka ne ya fusatar da ni, na mareta lta kuma tasa karfi ta cijeni, ta kuma gudo gida. Ina shirin biyota ne, sai ga ta da Hajiya. Anan ma Hajiya ta ci min mutunci kwarai da gaske.

Ku dakace ni

Daga taskar

Yar gidan imam KALUBALE BOOK 1 HABIBA ABUBAKAR IMAM (MRS ALIYU MAYERE)

Bismillahir Rahma Nirrahim