Page 81
wanda har ta tunzurani, na kasa daurewa, ni ma na shiga mayar mata da magana, saboda zahiri mallam na gaji da irin wulakancin da Haj take yi min, bata ganin laifin sameera akan komai, duk abinda ke faruwa tsakani na da ita, a wajen Haj nine mara gaskiya”. Ya numfasa, sannan ya ci-gaba da cewa "Don haka gaba daya na fuskanci aurena da Sameera akwai matsala, tunda mahaifiyarta na goyon bayanta, bata ganin laifinta. Don haka Malam ka yi hakuri, domin ina ganin zan hakura da ita.' Malam Jibrin ya numfasa cike da takaici, yace 'Musa ka yi hakuri don Allah kada ka tona min asiri, domin idan ka saki Sameera, na shiga tashin hankali, ka yi hakuri don girman Allah. Na san Sameera ba-ka jin dadinta, amma ka dubi girman Allah, kada ka saketa." Tausayin Malam Jibrin ya kama Musa yayi kasa da kansa yace "Malam ya wuce, zan ci-gaba da zama da ita, domin gain mutuncinka da kimarka." Malam Jibrin yace "Na gode, ka bar komai a hannuna, zan yi maganin abin, kada ka kara zuwa. Da kanta za ta dawo dakinta." Musa yace "To Malam na gode. Allah ya kara girma." Daga nan ya tashi ya zura takalmansa ya hau mashin dinsa, ya tafi, ya bar Malam Jibrin cikin tashin hankali da tunanin yadda zai yi da Hajiya Sa'a, domin dai ya san duk wannan koyinta ne da tarbiyyarta. A wannan ranar babu yaron da Malam Jibrin ya iya ba karatu, duk sallamarsu yayi, ya hade kai da guiwa. Yana neman mafitar KALUBALEN da yake ciki. Sai bayan sallar issha, sannan ya sami Hajiya Sa'a da Sameera a daki, wanda nan da nan Hajiya Sa'a ta turbune fuska. Malam Jibrin ya dubeta ya girgiza kai yace "Duk bata fuskarki ba zai hana na yi magana ba, ba kuma zai hana na yanke hukuncin da na yi ra'ayi ba". Ya lalubi wajen zama, ya zauna yana kallon Sameera yace "Ba tun yau na san cewa ke mutuniyar banza bace, ba ki da kirki. Yanzu ashe ba za ki yi hankali ba? Na rantse, Idan ba ki shiga hankalinki ba, za ki kai kanki, ki baro, rayuwa ma ka shuka alheri, ya ka kare, balle ka shuka sharri, ki na daukar aure tamkar wasa ko? To aure martabarsa da kimarsa ta zarce komai, kuma duk wanda ya wulakanta aure. sai Allah ya wulakanta shi. Ki kuka da