Page 82
Kanki ranar da duk Allah ya kamaki akan laifin da ki ke yima mijinki. Domin duk matar da bata bi mijinta ba, babu shakka makomarta jahannama. Sameera ina kwadayin ki zama matar kwarai, ki daina biye ma rudin shaidan,da kuma hudubar banza ta mahaifiyar ki,don mijinki bai da shi, bai kamata ki kwazzabe shi, ki hana masa sakat ba. Don me za ki maida mijinki tamkar wani abin kyama? Da samu da rashi duk na Allah ne. Kamar yadda arziki da talauci yake nasa. Yakamata, ki san abinda ki ke yi. Rayuwa ba haka take ba, ki zauna lafiya da mijinki. Musan guda nawa yake, da har za'a fidda rai da arzikinsa, ki ka san abinda zai zamo nan gaba a rayuwar? To ki yi hattara, Idan ba so ki ke ki zama abin tausayi ba, a ranar gobe kiyama". Ya nisa ya ci-gaba da cewa 'Da ace yau ban ba ki ilimi ba, da sai na yi kuka da kaina akan gurbacewar tarbiyyar auranki. Amma na ba ki ilimi. Sameera kin sauke Kur'ani, kin fahimce shi, kin karanci littafan addini, kin yi kuma illimin boko dai-dai gwargwado, to me yasa ki ke haka? Me yasa ki ka rufe idonki, ki ka take sanin da ki ke da shi?”, ya yi sa’a har ya kai karshen maganarsa Haj sa’a bata katse shi ba. Sameera jikinta yayi dan sanyi. Ta dago tana kallonsa tace "Baba ka yi hakuri." Ya giriza kai yace "Ni ba abinda ki ka yi min, mijinki shi za ki ba hankuri, ki kuma nemi afuwarsa." Anan ne Hajiya Sa'a tayi magana tace "A dalilin me za ta nemi afuwarsa." Ya daga mata hannu yace "Ba da ke nake magana ba, ban kuma gayyatoki cikin maganar tawa ba". Daga nan tayi shiru, tana ci-gaba da harare-harare. Malam Jibrin yace “Yanzu karfe takwas da rabi na dare, ina me umartarki da ki tashi, na yi miki rakiya zuwa gidan mijinki, ki koma dakinki, domin ba na bukatar ki kwana min a gida." Hajiya Sa'a tayi wuf! Tace "Ta tashi ta koma ina? Haba Malam, ba dai ina kallo ba. Musan me? Ai Sameera ta gama zama da Musa, babu sauran wata alaka a tsakaninsu, ina ba zai yuwu ba". Malam Jibrin ya kafe idanunsa masu cike da fusata akan Hajiya Sa'a yace "Na rantse da Allah, yau Sameera bata kwana a gidan nan, sai gidan mijinta, ba ki isa ba Sa'a, ni ma ina da iko akan yata". Hajiya Sa'a ta tashi tsaye tana fiddo idanu waje sai kace tsohuwar mayya tace, "Ni ma ina da iko a kanta, ni da na sha wahalar haihuwarta, ban haifi jaka