KALUBALE BOOK 1

Page 83

by @yargidanimam

ba Da Musa zai sa min ita a gaba da duka, ba inda za ta koma, domin goben nan zan maka kararsa a kotu, dole ya bata takardarta. Aure an gama shi" Malam Jibrin ya nunata da hannunsa yace "Sa'a na gaji da halinki, na gaji, to ina tabbatar miki da cewa matukar Sameera bata koma gidan mijinta ba, to ke ma sai dal ki kwana a gidan naki Iyayen domin na kai makura a kan bakin halinki". Tasa masa ido tace 'Me kake nufi? Yace "Ina nufin abinda kike son ya sami auran Sameera, ke ma zai sami auranki, kuma ina nufin hakan har cikin zuciyata, ba wai ina fada haka nan bane". Jin haka yasa Sameera ta tashi da sauri ta dau gyalenta, ta dubi Haj Sa'a da tayi tsaye, bata da bakin magana tace "Hajiya na koma, sai da safe." Bata lya cewa uffan ba, har Sameera ta fice. Dama in ka ji ki gudu, ya kafe. To tabbas sa gudu ne bai zo ba. Malam Jibrin ya saki tsaki ya bita a baya. Tun daga gidansa har gidan Musa. Nasiha yake ma Sameera tare da jan hankalinta akan zaman aure, to tamkar dai Sameera ta ji, ta dauka, domin a kofar gidan Musa. Malam Jibrin yace "Idan kin shiga, ki nemi afuwarsa akan fita da ki ka yi, bada izininsa ba, ki kuma roki afuwar maganganun da ki ka gaggaya masa". Tace "To Baba, na ji, na gode." Sai da ya ga shigarta cikin gidan Musa. Sannan ya numfasa ya kamo hanyar gida, zuciyarsa cushe, yanzu yaya zai yi da halin Hajiya Sa'a? Yanzu kullum sai dai ya zama Alkali a tsakanin 'Ya'yansa? Tarbiyyar daya ba Ya'yansa, duk ta rushe. Yau da ace Hajiya Sa'a ta haifar masa 'ya'ya da yawa, daya shiga uku. To Allah ya takaita, suke nan su biyu. Daga Sameera sai Haneefa. Babban danta ya rasu, me bi masa, ya rasu , Daga nan ta dade bata kara haihuwa ba, sai akan Sameera, tsakanin Sameera da Hanefar ma da tazara, tun daga kan Haneefa bata kara haihuwa ba, kila wannan shine dalilin da yasa ta dauki son duniya ta dora musu.Wanda yasa bata kaunar ganin bacin ransu ko wahalarsu, Kullum cikin kokarin kwato musu 'yanci take. Amma kuma ace 'yanci kuwa? A ganin Malam Jibrin dai wannan ai son banza ne, tunda tana neman ta watsa su ta kuma raba su da darajarsu, wato gidan auransu, tunda mace bata da wata daraja, sai a dakin mijinta,