KALUBALE BOOK 1

Page 84

by @yargidanimam

Amma lalle yakamata Hajiya Sa'a ta san Annabi ya faku, Haka ya kasance cikin wannan tunanin har ya kai gida, koda ya shiga gidan ma bai bi ta kan Hajiya Sa'a ba, dakinsa yayi shigewarsa cikin bacin rai. Yana kishigide kan gadonsa. Hajiya Sa'a ta shigo dakin babu ko sallama ta tsaya a bakin kofa tace "Ka mayar da ita, idan kasheta ma zai yi, ya kasheta, ba-ka da asara, da ace ba-kai ka haifi 'Ya'yan nan ba, da sai nace ba-ka kaunarsu, amma babu komai. Haka al'amarin duniya yake... Malam Jibrin yace yana dubanta 'Sa'a saninki bai yi miki amfani ba, babu abinda saninki ya kareki da shi, ki na 'yar Malamai wacce ake alfahari da mahaifinki a duk fadin Najeriya, amma ki zauna ki na yin abinda kungurmar jahila ba za ta yi shi ba. Na rasa abinda ke damunki. Yan 'Ya'yan guda biyu da Allah ya bar miki, maimakon ki tsaya ki gyara musu rayuwa, a'a kin dauki mummunar akida, ta son hutu da son abin duniya, kin lika musu, yadda ki ke tafiyar da auranki, haka ki ke son su tafiyar da tasu, Bayan kin san ke kanki ba dai-dai kike aikatawa ba". Tace "Ai dama ni kullum a hakan nake a gunka, ba na daidai... Ya daga mata hannu. "Kada ki dameni, ki koma dakinki. Sameera dai na maidata gidan mijinta kuma daga yau ba na bukatar ki kara zuwa gidan Sameera. Ta fiddo idanu waje cike da mamaki tace "Ni din kada na kara taka kafata gidan Sameera? Ya gyada kai 'Eh, haka nace, idan kuma ki ka je, to bada yawuna, ba kuma da yardata ba, bada kuma izinina ba". Za ta yi magana kenan, yayi saurin dakatar da ita, ta hanyar rokonta da Allah da Annabi tayi hakuri ta bar shi ya sami natsuwar zuciyarsa, cikin tsananin fusata ta fice fuuu! Kamar za ta tashi sama. "Kai jama'a! Mata kenan! Shi yasa kullum ake kira mana rashin hankali, abinda bai taka kara ya karya ba, sai mu maida shi wani babban abu na hayagaga da tashin hankali, saboda rashin hakuri irin namu. Allah ya kyauta, yasa mu gane, ya kuma ba mu ikon gyarawa.