KALUBALE BOOK 1

Page 85

by @yargidanimam

Kwanci tashi, asarar me rai. Yau ga shi har Muhseen Usman Jigawa ya kammala koss din daya kawo shi Kaduna, garin gwamna, mako biyu kawai aka dibar musu su koma Delta. Ainihin wajen aikinsu. To a ranar juma'a, a ranar Umar yayi Katsina. Shi kuma Muhseen yayi Jigawa, tunaninsa daya da fatansa shine Allah yasa ya kare mako biyun nan lafiya, ba tare daya sami matsala daga Haneefa ba, domin ya san tun auransa da ita bai taba yin mako biyu tare da ita ba, tun bayan gama cin amarcinsu. Tunaninsa daya, shine ya ga ko kwana daya yayi, sai sun yi fada da Haneefa balle mako biyu. To ya dai isa Jigawa lafiya, cikin murna da farin-cikin kammala kos dinsa. Amma Hajiya Goggo bata fuska tayi a lokacin da yake gaya mata batun kammala kos din nasa tace "Yanzu shi kenan Magajin Malam nan da mako biyu zaka kara yin nisa damu, wanda ganinka sai an wahala, zuwanka kuma sai wani dogon lokaci? Yayi dan murmushi yace "Hajiya to ya za'ayi? Tunda na riga na zabar ma kaina haka, sai dai hakuri kuma a dinga daurewa ana yi mana uzuri, domin tabbas dole za' a sami bambanci". Hajiya Goggo ta numfasa tace "To Allah yayi mana jagora". Ya jima tare da Hajiya Goggo kafin ya dawo gidansa, ya sami tattali daga Haneefa, a wannan daran sun biya ma juna hakkinsu tamkar abin ya dore a haka, domin shi kansa Muhseen yadda Haneefa ta tafiyar da shi, ya sami zuciyarsa cikin sukuni. A cikin makwanni biyun nan. Muhseen ya je gida jen 'Yan- uwa da abokan arziki ya sada zumunci. Haka zalika ya sami kansa da jindadin zamansa a Jigawa, a dalilin samun kulawa daga Haneefa, domin hatta zuciyarsa ta fara karkata akan kaunar Haneefa. Dama shi mutum yana son me kyautata masa ne, komai muninsa, yana kuma kin me munana masa, komai kyawunsa. Addu'ar Muhseen daya ce. Allah yasa Haneefa ta dore a haka, tunda al'amarin nata wani lokacin tamkar me juju ce, amma kam! Da za ta dore da hakan, hakika da ta taimaki kanta ta hanyar mallakar zuchyar Babban Yaya, dan mutan Jigawa. To kayya dai! Domin dai kwanansa goma a Jigawa. Ranar litinin bayan fitowa daga sallar azahar. Muhseen yana kishingide