Page 86
akan doguwar kujerar Hajiya Goggo. Shi da ita ne suke hira. Hajiya Goggo ta dan dube shi tace "Magajin Malam yakamata idan za ka tafi, ka aje ma Haneefa wadatattun kudi wadanda za su isheta komai, ba tare da ta nema ba, bayan tafiyarka." Cikin rashin fahimtar maganarta ya dan dago da kansa yana kallonta yace "Hajiya ban fahimci maganarki ba? Ai ko ina bar ma Haneefa kudi masu kauri wanda za ta iya yin duk abinda ta ga dama, don dai bukatarta ita kadai ko akwai wata matsalar ce?" Hajiya Goggo ta jinjina kai tace "Ban san hakan ba, na dai yi tunanin da kana bar mata, da bata dinga yawan amsar kudi a hannuna ba, da sunan ka ce ta karba, kafin ka dawo". Wannan karon tashi yayi ya zauna, yana kallonta sosai yace "Hajiya, don Allah gaya min, idan banda kudin anko dana kiraki a waya nace ki bata, tun wancan komawar tawa, to ni ban sa ta kara amsar wasu kudin a hannunki ba". Mamaki ya cika Hajiya Goggo ta tsare shi da ido tace "Magajin Malam Haneefa ta amshi kudi a hannuna da kuma wanda na ranto a dalilin ba ni da shi a lokacin za su kai Naira dubu dari da goma". Dif! Muhseen yayi yana ci-gaba da kallon Hajiya Goggo, baki sake cike da mamaki da jin haushi mara misaltuwa, ya kasa cewa uffan, illa tashi da yayi tamkar wanda aka tsikara ya fice. Hajlya Goggo na kiransa, amma ko juyowa bai yi ba. Haneefa na zaune a kasan kafet tana shirya littafanta na hausa da tayi kwalemarsu. Muhseen ya shigo cikin fushi da fusata, ta daga kai cikin fara'a ta dube shi, ganin fuskarsa cikin wannan yanayin, yasa ita ma ta hade tata fuska, ta sha mur, tamkar za ta fasa ihu. Cikin dakewar murya tace "Lafiya za ka shigo, kana wannan hade ran sai ka ce wanda aka daka, aka saki". A fusace yace "Wai ke Haneefa wace irin mace ce ke, kin ko san abinda ki ke yi? "A'a ba zai yuwu ka rufeni da fada ba tare dana san abinda na yi maka ba, gaskiya". Ya hadiye zazzafan yawun bakinsa, yace "Me ki ka yi da kudi har dubu dari da goma, me yasa ki ka karba a hannun Hajiya, me ki ka rasa