KALUBALE BOOK 1

Page 87

by @yargidanimam

meye ban aje miki ba, da za ki yi min irin wannan cin mutuncin, me ki ka yi da su?- Haneefa tace "Au saboda haka ne za ka zo ka na yi min irin wannan fadan? To ina cikin bukata, don ka'aje min kayan abinci, ka ba ni dubu ashirin, sai aka ce maka zan rasa yin wasu bukatun nawa? Me dubu ashirin za ta yi min a cikin sati uku? To ni kada ka kara min fada, don ba wani abu na yi da su ba, cikawa na yi na sai babban injin saka." Galala yayi yana kallonta har ta tashi tana yi masa wani irin kallo, tace "Laifi ne, don na amsa a hannunta? Idan ba' a gunta ba, wajen wa zan je na amsa? Ni kada ka kara yi min fada, don ban ga dalili ba". Daga nan bata saurari komai ba, ta juya ta bar falon tana kunkuni. Muhaseen ya fada kan kujera yana maida numfashin bacin rai .ya kudundune idanunsa. Shin ya zai yi da Haneefa? Wata zuciyar ta ba shi shawara me kyau akan kada ya biye mata, ya kuma shawo kan bacin ransa. Ya jima kan kujera zaune bakinsa na fadin "Inna- lillahi'wa-inna ilaihirraji'un! Wanda hakan shi ya taimaka wajen daidaita hankalinsa waje daya da kuma gusar da bacin ransa. Sai da aka kira sallar la'asar, sannan ya fita zuwa masallaci, bayan dawowarsa daga masallaci, dakin Hajiya Goggo ya yada zango, tana jin shigowarsa. Ta fito daga uwardaka, tana kallonsa tana kokarin gano abinda ya faru, bayan shigarsa wajen Haneefa. Amma bata gane komai ba, domin dai Muhseen yayi kokarin boye duk wata damuwarsa. Cikin murmushi yace "Hajiya zan sami fura a wajenki? Tayi murmushi ita ma tace "Akwai ragowar wacce Malam ya sha, ya rage, a kawo?" Ya lumshe do ya bude yace "A kawo Hajiya, wa zai ki sidin Malam? Tayi dariya gami da ficewa, bata jima ba, ta dawo dauke da kwanon furar ta mika masa, ya amsa har za ta wuce, ya dubeta yace "Zo ki ji Hajiya". Ta dawo da sauri ta zauna kusa da shi tana kallon kyakkyawar fuskarsa tace "Ya aka yi ne Magajin Malam? Ya dan kurbi farar, sannan ya tsagaita yana kallonta yace "Don Allah daga yau kada ki kara ba Haneefa ko kwandala, domin ina iya kokarina wajen tabbatar mata da duk abinda za ta bukata