KALUBALE BOOK 1

Page 88

by @yargidanimam

ban yi zaton ko wata shida na yi ban dawo ba Haneefa za ta shiga damuwar rashin wani abu ba. Ra'ayi ne kawai yasa ta karbar wadannan kudin". Hajiya Goggo ta dan nisa tace "To shi kenan, dama ni na ga babu yadda za'ayi ta tambayeni abu da sunanka, na hanata ne, amma tunda ka fadi haka, shi kenan". Daga nan bai kara cewa komai ba, ya ci-gaba da shan furarsa har ya koshi, sannan ya aje ya koma ya kwanta, ya maida idannusa ya rufe tamkar me shirin yin barci. Tun daga wannan ranar zaman lafiyar dake tsakanin Muhseen da Haneefa yayi kaura. Domin dai Haneefa tuni ta fita harkarsa, shine ma ke kokarin yi mata magana tare da nuna mata komai ya wuce. Amma Haneefa ko a jikinta, fushi take sosai ta ki hucewa. Daran da washegari zai koma bakin aikinsa a Delta, ya aje Haneefa a gaba tana zaune akan gadonta, shi kuma yana zaune kan durowar gadon yana yi mata magana cikin taushi da sayin murya yace 'Haneefa gobe da asuba Insha-Allahu zan koma wajen aikina a Delta, wanda kin san cewa dama Kaduna koss ne ya kawoni, ainihin wajen aikina, na Delta, kin san kuma Delta ba nan bace, akwai matukar nisa, yadda ba zan iya jure dinga dawowa kamar yadda nake dawowa daga Kaduna ba. Kin kuma san sha'anin aikinmu, akan dade kafin mu sami izinin dawowa gida, don haka dole a yanzu za'a sami sauyi da banbancin wanda nake fata da addu'ar ki yi hakuri, ki jure ki sani, duk inda nake, hankalina na wajenki" Yayi shiru yana kallonta, ganin bata da niyyar yin Magana, yasa ya ci-gaba da cewa "Na yi kokarin cika miki (Store) da kayan abinci, domin ba ni da fargabar ace ko nan da watanni bakwai na yi, ban dawo ba, za ki nemi wani abu, Sai dai ina fatan ki daure, ki dinga kula da kyau, kada ki dinga almubazzaranci da kayan abincin, don kin ga akwai", Anan ne ta dago ta dube shi tace "Dama ai sana'ata kenan almubazzaranci". Ya girgiza kai "Ni ban ce ba, don Allah ki yi hakuri mu rabu lafiya, ba na son irin wadannan furucin naki." Ta maida kanta kasa tana motsa baki, ita ta san abinda take fada. Muhseen ya