Page 89
Jinjina kai ya ci-gaba da cewa "Zai iya yuwuwa na dade, ban dawo ba, sai dai ina fata koma meye za ki dinga yi min uzuri." A hankali tamkar bata son yin magana tace "Na ji. Allah ya kaika lafiya". Ya jinjina kai gami da miko mata Naira dubu arba' in, yace "Ga dubu arba'in ki rike a hannunki, ba na bukatar ki amshi ko kwandala a wajen wani.” Tasa hannu ta karba tace "Na gode". Karo na farko kenan da tayi masa godiya, akan duk wata hidima da yake mata, ya kuma ji dadi. Haka zalika, duk kauda kanta da take. Muhseen sai da ya biya bukatarsa da ita, domin baya bukatar ya tafi da sha' awa, ko ita ya tafi ya barta cikin sha'awar. Washegari kuwa tun fitowa daga sallar asubah. Muhseen yayi sallama da Haneefa da jama'ar gidan Sheik Sadisu. Hajiya Goggo har da matsar kwalla. Daga nan Muhseen ya dauki hanyar Delta cikin tunani da sake-saken halayyar matarsa,
Yau Alhamis Haneefa gidan Sameera ta wuni, daga gidan Sameera, sai tayi gidansu tayi matukar Sa'a Malam Jibrin baya nan, don haka ta sami sakewa, Hajiya Sa'a ita ma ta ji dadin zuwanta. "Ai daga gidan yaya Sameera nake." Hajiya Sa'à ta saki tsaki tace "Bari kawai, ai Sameera tana cikin ukuba, wacce ubanta ne sila, tunda shi ya hana na kashe auran". Haneefa ta nisa tace "Ai duk ta gaya min abinda ya faru, gaskiya Yaya Sameera tana bukatar agaji, ko kin san ba don zuwana ba, sai dai ta wuni haka nan, kila ma kwana za ta yi babu abinda za ta ci, shine na dibar mata taliyar dana taho miki da ita, na bata har biyar, to na dai barta za ta dora, amma na yi mata gargadi, ko ta dafa, idan ta ba Musa, ban yafe ba". Hajiya Sa'a tace "Yauwa, to Allah yasa ta ji, don ba abin mamaki bane tana gamawa, ta zuba masa ba, don ita ma din wani lokacin ba tunani gareta ba” yanzu ko abinda za ta ci bata da shi?". Haneefa ta tabe baki tace "Abin Wallahi gwanin ban tausayi, gaskiya Musa yana zaluntarta, shi Baban bai sani bane.? Hajiya Sa'a tayi tsaki "Idan ya sani ma, menene, tunda babu abinda ya dame shi, harkarsa kawai yake, bai damu da farin-cikinku ba, nice dai na damu da ku, “ ta janyo ledar kayan abincin tace “me aka kawo mana”, ta yi murmushi tace “ dan kayan abunci ne Haj “, ta shiga tone ledar tana sa mata albarka daga bisani ta tashi tana fadin “bari na adana su kafin babanki ya shigo ya gani ya kwana ja min aya da hadisi, aje kayana nake idan ta bada kudin da zaa saya, sai na kalmashe kudina na fito da shi a matsayin sayowa na yi”. Haneefa tayi dariya tace “lalle Haj “. Itama daki ta shige da kayan tana dariya.