Page 90
Tsawon makwannni hudu kenan da dawowar Muhseen Delta, ya sami kwanciyar hankali da natsuwar zuciya, gidaje ne nasu na musamman inda suke zaune, su uku ne, a nasu gidan. Daga Muhseen sai Umar, sai Kassim, wani dan Gombe. Muhseen shi ne ke ja ma musulman wajen sallah, ko yaya ba sa sake da lokacin sallah. Haka zalika wasu da yawa daga cikinsu masu sha'awa, bayan sallar issha'i, su kan dauki karatun Kur'ani a wajen Muhseen, domin fahimtar da suka yi Muhseen yana da ilimi, hankali da cikar kamala. Kuma duk girman mutum bai wice ya nemi ilimi ba saboda haka a aje girman kai a nemi ilimi , , wannan dabi'ace me kyau sosai. Domin duk inda mutum yake, bai kamata ya manta da tambarinsa.na musulunci ba, kamar Muhseen, komai rintsin aiki, baya mantawa da ambaton Allah. Rayuwa irin ta shi, tana da kyau, a bar koyi ce a gun kowa. Magana da yawan surutu, ba su dame shi ba, shi yasa abokan aikinsa da yawa za ka ji suna kiransa da Malam. Tsawon wannan lokacin, kullum sai yayi magana da Haneefa a waya, domin maganar gaskiya baya son ya ji ta cikin damuwa,
Ku dakace ni
Daga taskar
Yar gidan Imam KALUBALE BOOK 1 HABIBA ABUBAKAR IMAM (MRS ALIYU MAYERE)
Bismillahir Rahma Nirrahim