KALUBALE BOOK 1

Page 91

by @yargidanimam

Yana son ya dinga sauke nauyin daya hau kansa, domin ya san matsayi da martabar aure! Shi yasa ko meye, da ta fara korafi, zai nemi afuwarta, ya kuma bata hakuri, domin bayan neman duk wani abu da zai ja masa sabani da matarsa, wacce yakamata ace ya mutunta, fiye da kowa a duniya. Haka zalika Hajiya Goggo da Sheik Sadisu su ma kullum sai Muhseen ya ji lafiyarsu, kuma hakan ne kawai yake dasa masa kwanciyar hankali

Watanni biyu cif! Sannan Muhseen ya je jigawa, a dalilin wayar da yayi da Haneefa ta tabbatar masa bata da lafiya. Ya sameta da sauki, sai dai tana kwance, sai ya ga Haneefa ta kara masa kyau, ta kara haske, ta kuma kara cika kusa da ita, ya zauna sosai, gami da kamo hannayenta ya rike, yana kallonta. Yace "Me yasa ki ka ki yarda ku je asibiti? Hajiya ta ce min tayi-tayi dake ku je asibiti, amma kin ki, to me yasa Haneefa, ko ba ki damu da ciwon bane ko kuma don kin ga ciwon ya kara miki kyau ne, shi yasa?" Ta dago tana dubansa tace a hankali "Kai nake jira, na gaya maka irin ciwon nawa, sannan mu tafi asibitin,” Muhseen yasa mata ido yace “tunda kinsan irin ciwon da kike yi ai sai kije asibiti babu dalilin da zaki ce dole sai na dawo sannan zaki je asibiti”Ta yunkura zata tashi , ta kasa, ya kamota ya zaunar da ita, suna kallon juna, sannan tace "Ciki gareni!" Muhseen ya fiddo idanu waje, cike da farin ciki da wani irin jin dadi dake sanyaya zuciyarsa yacc "Ciki Hanefa? Ya riko hanmunta ya kura ma cikin idanunta ido, rana ta farko kenan da ya sami zuciyarsa da jin son Haneefa . Muhseen duk kauda kansa, yana matuka son yara, duk miskilancinsa, in dai ya ga yaro, sai ya kula shi, to yau ya zai ji a zuciyarsa? Ace ya kusa mallakar dan kansa? A tausashe ya kira sunanta 'Haneefa kin gama min komai, ba ni da bakin da zan yi miki godiya, amma lalle kullum zan kasance me yi miki addu’ar sauka lafiya”Hañeefa ta jinjina kai tace "Amma ina reman wata alfarma guda daya a wajenka ko nace ina son ka amince min".