KALUBALE BOOK 1

Page 92

by @yargidanimam

"Menene fadi, ko meye kanwata." Cewar Muhseen Haneefa ta dago tana kallonsa, sannan kamar daga sama ya ji tace "Ina bukatar mu je asibiti a zubar min da cikin nan",. Komai dif! Yayi ma Muhseen, ya kafeta da ido, yana kokarin ya gasgata abinda kunnensa ya ji masa "Mene ki ka ce?" "Ka ji abinda nace, babu bukatar na maimaita." A sanyaye yace "Meye hujjarki na cewa azubar da cikin? “ ya tambayeta cikin matukar fusata.Ta Gyara zamanta tace "Kwata-kwata da auranmu bai wuce shekara daya da rabi ba, a tunanina, na yi saurin samun ciki, kuma ba zan iya jure ma wannan laulayin ba, ina matukar wahala, haka kawai. Bugu da kari, duk duniya, idan akwai abinda na fi tsoro, bai wuce mutuwa da haihuwa ba, ina masifar tsoron haihuwa, don haka nake bukatar azubar da cikin". Gumi ya keto ma Muhseen, wanna wace irin masifa ce! Menene kuma wannan? Anya Haneefa tana da hankali kuwa? Nan da nan idanunsa suka yi jajir! Tunda ya zo duniya, bai taba samun bacin rai irin wannan ba, cikin sarkewar murya yace "Haneefa na dade ina tunanin ba kya so-na, amma a yau na tabbatar da hasashena. Ba kya so-na, tunda duk wanda baya kaunar aje zuri'a da kai, to ba masoyinka bane, kin kuma ba ni tsoro da mamaki, kin ko san hukuncin zubar da ciki.? To zubar da ciki, ba shi da banbanci da kisan kai, kuma ban taba zaton haka daga gareki ba, kin ba ni kuhya Wallahi". Haneefa tace "Eh na ba-ka kunya mana, tun da ina kokarin na tsira da raina da lafiyata, tunda kuma ka ga ba kai ne kake shan wahalar da nake sha ba, idan kuma haihuwar ta zo, ba-kai ne za ka yi min ba, dole a zubar da cikin nan Malam. Don ban shirya haihuwa yanzu ba". Muhseen ya fusata kwarai, ya tashi yana kallonta yace "Na rantse da Allah akan wanna maganar, ina iya rabuwa dake, kuma ina tabbatar miki da cewa daga yau har zuwa ranar da za ki haihu duk abinda ya sami cikin nan. Ke ce, kuma ba zan ji tsoro ko shakkar maka kararki a Kotu ba, duk yadda nake dake, don kada ki dauka ko tsoronki nake ji, yasa na ke ja da baya tare da raga miki, akan duk irin cin kashin da kike min, ni ma akwai zuciya a kirji na kuma. sanin darajar aure da sanin darajar mace yasa nake raga miki.