KALUBALE BOOK 1

Page 93

by @yargidanimam

Amma wannan karon ba na kyashin kowa ma ya san halin da nake ciki dake, domin ni ne mutum na farko da zan fara gabatar da maganar, kuma a gaban duka danginmu, wato ranar taronmu" Yana gama fadin haka, ya juya fuuu! Har ya kai kofar daki, ya juyo yana kallonta yace "Da na san abinda zan tarar kenan, idan na dawo, da ban zo ba, kuma duk abinda ki ke min kanki ki ke ma". Daga nan ya fice cikin tsananin bacin rai da tashin hankali. Haneefa tayi turus! Nan da nan ita ma ta ji zuciyarta ta cushe da rashin jin dadi, maganar gasklya ba wai cikin bane bata so, tsoron haihuwa take kwarai da gaske, tun tana karamarta, da zaran ka ce mata za ta haihu, za ta rushe da kuka. To amma wannan ai aikin banza ne, tunda haihuwar ta zama dole, kuma hauka ce babba da jahilci, ki dubi tsabar idon mijinki, ki ce za ki zubar masa da ciki, domin duk son da yake miki, daga wannan ranar da ki ka ce za ki zubar masa da ciki, ba zai kara yi miki kallon daraja ba. To ya ma za'ayi, banda shashanci da, da ubansa, ki ce za ki zubar. Ai ko shege ne, bai halarta ki zubar da shi ba. Wasu dai matan gaba daya tamkar ba mata, ba babu kirsa, ba iya Magana, ba iya jan hankalin miji, balle ki zama '"yar gaban goshinsa, yanzu ko komai ya canja mata, sai da kirsa da iya salo, idan ba haka ba, ki na ji, ki na gani, za ki ga an kwace miki mijin, tunda shi namiji, duk shekarunsa, duk tsufansa, tarairaya yake so, da kulawa da Lafazi me dadi. Amma me ake da mace, me irin hali da dabi'ar Haneefa, ba don ma ta sami miji me tsoron Allah da hangen nesa ba, da ta Shiga Magana, to ana sonka ma, ka shuka Irin wannan dabi'ar. An Juya maka baya, balle irinsu Haneefa da take a jone, ko don bata San hakan bane, to koma dai menene? Yakamata ayi hattara! Har gari ya waye. Muhseen bai kara neman ma inda Haneefa take ba, balle yayi mata Magana. Haka zalika ko Hajiya Gwaggo bai gaya ma ba. Washegarin ko da sassafe ya kwashi hanyar delta, bayan yayi sallama da su Hajiya Goggo. Amma ko fuskar Haneefa bai gani ba. Balle yayi mata sallama. Ya dai aje mata sakon takarda kan kujerar da tafi zaman kallo a kanta. Lalle Haneefa ta tuke