KALUBALE BOOK 1

Page 94

by @yargidanimam

Muhseen. Abinda ita ma ta fada kenan a lokacin da ta ga takardar daya bar mata. Zaunawa tayi sosai kan kujera, tana karanta sakon nasa. Haneefa! "Ina nan akan rantsuwata, matukar wani abu ya sami cikinki, na hakura dake a matsayin matata, kuma sal mun tsaya a gaban Alkali, kafin mu je babbar kotun Ubangiji. Na zo da nufin kasancewa dake, amma na yi da na sanin zuwa, kuma na koma ban San ranar dawowata ba. Amma ki kula, ki kuma lura, ina son abinda kre cikinki, fiye da komai a rayuwata. Abdul-Muhseen! Haneefa tayi jagwaf! Akan kujera, tana da na sanin abinda tayi, yakamata wani abin kunya, sai ta sami kanta da addu' ar Allah ya tsare mata cikinta. Allah yasa kada wani abu ya same shi, domin ta ceci auranta, don dai ita kanta ta san tana son auranta, tana kuma son Yaya Muhseen, matukar so, bata fatan wani abu ya sami tinkahonta, wato auranta. A da ta ki yarda Hajiya Goggo ta fahimci tana da ciki. Amma tun bayan tafiyar Muhseen. Wani abin ma da gan-gan take, don dai Hajiya Goggo ta gane tana da ciki. Har wata biyu ya shiga na uku, nan da nan ko Hajiya Goggo ta gane inda Haneefa ta dosa. Murna da doki, ai ba'a Magana, a wajenta domin, dai gaba daya ta dawo da Haneefa dakinta, tare suke kwana, tana kulawa da ita da bukatunta, bata akin fari, balle na baki, sai aikin rainon ciki. Duk dangi, cikin kankanin lokaci babu wanda bai san Haneefa tana da ciki ba. Ita kanta Hajiya Sa'a ta fi kowa murna, domin dai haihuwar Haneefa wata hanya ce ta kara kama Muhseen a hannu, kuma Haneefa za ta kara samun daukaka a cikin dangi, ta kara tabbatar da hakan ne a lokacin da ta je gidan, ta ga yadda Hajiya Goggo ke ji da Haneefa. Sai abinda ta ga damar ci, ta ke ci. Tana daga kwance ake yi mata komai. Ta kara kyau da kiba, kowa tattalinta yake. Wannan abu ya fi komai dasa farin ciki a cikin zuciyar Hajiya Sa'a.