Page 95
Muhseen bayan komawarsa Delta, ko Umar bai gaya ma bakin kudirin Haneefa ba, domin a ganinsa wannan abin kunya ne, ace matarka za ta zubar da cikin da yake tabbas naka ne, don haka ya kunshe bakinsa, sai dai abin ya ci-gaba da damun zuciyarsa, da ya ga zai shiga aikinsa ne, yayi kokarin fitar da abin a zuciyarsa. sai dai yayi alkawarin matukar ta aiwatar da abinda tayi niyya, zai rabu da ita. Koda hakan na nufi wargajewar zumuncinsu ne. Haka zalika tun bayan dawowar tasa, bai nemi Haneefa a waya ba, sai dai kullum idan ya kira Hajiya Goggo, tace ga matarka nan kusa da ni, kuma duk da haka, baya cewa ta bata wayar. Hakan ya tabbatar ma da Haneefa cewa Muhseen yayi fushi da ita, fushin da bai taba yin irinsa ba a kanta. Haka rayuwa ta ci-gaba. Ubangiji na sarrafa komai yadda ya ga dama, yana kuma tafiyar da komai a bisa tsarinas, sai da Muhseen ya kwashe watanni uku, sannan da kyar ya sami izinin zuwa gida. Kwana uku kacal! Ya samu, a dalilin matsanancin aikin da suke ciki. Cikin fargaba ya iso gida, fargabar da bata wuce ko Haneefa ta zubar da cikin ba? Amma abu ma fi dasa farin-ciki a Zuciyarsa, shine ganin Haneefa da katon cikinta a gaba, wanda Yayi mata matukar kyau, tana kwance akan kujera a dakin Hajiya Gwaggo.
Muhseen na daya kujerar a zaune. Hajiya Goggo na kusa da shi, duk a dame take, tana yi masa tambayar dalilin ramarsa. Muhseen yace "Daga dawowata, duk ki na neman ki damu kankiI, don kin ga rama a jikina? Wannan har wani abu ne? Kada fa ki manta, ina nisan duniya, ina da bukatar na dinga jinku koyaushe, amma ba dama, dan taron dangin dana saba halarta na sangarce da zuwa, lokacin, ina Kaduna yanzu, sai dai ace oh yanzu ana can ana taro, ba ni da halin zuwa, ba ni da Wani lokacin kaina, to ba dole na yi rama ba, Hajiya." Ba Hajlya Gwaggo ba, hatta Haneefa ta tausaya masa, duk shiru suka yi, suna Dubansa.