Page 96
Daga bisani Hajiya Gwaggo ta dubi Haneefa tace "Yau sai ki koma dakinki, tunda mijinki ya dawo, aje can shi ma ayi masa shagwabar, ko na samu na huta." Muhseen yayi murmushi yace "Au Hajiya ki ce takura miki take? "Ga ta nan kam! Ka je kai ma ka ji. Ba zance maka komai ba." Haneefa ta dago tana dariya tace "Oho! Dadin dai abin ke ce nan ki ka gayyatoni, sannu Allah. Sannu Annabi, yanzu ko ba ki koreni ba, tafiya zan yi, tunda mijina ni kadai, ya dawo". Ya ji dadin maganarta, don haka ya bude ido sosai, yana kalionta. Hajiya Goggo tace "Oho a dai daina cika baki, kwana nawa zai yi Ya tafi, ya barmu tare." Haneefa ta tashi ta mike da sauri, saura kadan ta fadi, cikin Firgita Muhseen yayi gaggawar cafe matarsa. Hajiya Goggo ta iso gabansu cikin firgita "Yaya Magajin Malam, ba komai ko? Ya kara riketa sosai, yana dubanta yace "Allah ya takaita Hajiya, ba komai". "Allah ya kyauta, batun yau nake gargadinta da ta dinga kulawa ba, ta kuma kiyayi yin abu cikin karfi". Daga bisani dai Muhseen ficewa yayi rike da matarsa zuwa gidansu. Sai da suka kai tsakiyar falon gidan, sannan ya saketa, ya tsaya yana kallonta har ta dan ji kunya, ya kasa jurewa yace "Haneefa cikin nan yayi miki matukar kyau, ba zan taba gajiya da kallonki ba". Ta tako a hankali zuwa gabansa, daga bisani duk suka zube kan kujera. Hanefa na dubansa a kunyace tace. "Na gode, amma ina neman afuwarka a bisa abinda ya faru". Ya kama hannunta ya rike, yana murzawa yace "Dama wauta ce da rashin hankali, ke dawainiya dake, a lokacin. Amma tunda kin gane kuskuranki, shi kenan, ni ganinki da cikin nan ma, ya tilastani mantawa da komai. Haneefa ina son yara, ina son cikin nan" Tana jin dadin maganar tasa, ya kara kallonta "Allah ya saukeki lafiya". Shiru tayi tana kallon idanunsa, domin tana jin dadin ganin kulawa da kaunarta a idon nasa. Tsawon kwanaki da Muhseen yayi tare da matarsa, ba su yi fada ba, to me ma zai sa su yi fadan? Tunda bakinta ya rufe da irin tattali da nunin kauna da Muhseen ke mata, ita me cewa Muhseen bai iya soyayya ba, sai gashi a cikin kwana ukun nan, ta yardarma kanta Muhseen shine gwarzon masoya.