Page 97
Hakika wannan cikin ya kara mata kima da martaba. Haka zalika wannan shine karo na farko da lokacin komawar Muhseen yayi, ya sami kansa da rashin son komawar, sai da ya kara kwanaki biyu, sannan ya koma. Zuciyarsa cike da tunanin Haneefa da cikinta, dama shi so a hankali yake shiga. Muhseen kam! Ya yarda da hakan, domin dai da kansa yasan soyayyar Haneefa ta sami waje a zuciyarsa, domin dai a yanzu idan yace kwata-kwata baya sonta, to yayi karya kuma duk a dalilin cikin jikinta ne , domin idan don ta halin Haneefa ne babu wanda zai so ta.
Haneefa dai na cikin kulawa, har lokacin haihuwarta yayi. Ranar laraba ta tashi da nakuda, a da Hajiya Goggo ta so ta haihu a gida, amma Sheik Sadisu ya bada umarnin a tafi asibiti, abin ya zo mata da sauki, domin ba su fi minti talatin da isa asibitin ba. Haneefa ta haifo kyakkyawar "*yarta me kama da ubanta. Batun murna wajen Yan-uwa, ai ba'a Magana, domin kafin ka ce meye wannan? Har asibitin ya cika da Yan-uwa da abokan arziki, hatta Hajiya Hadeeza, aje kunyar tayi yau a gefe, domin har da ita a gyara Haneefa, ita ma Hajiya Sa'a baki ya kasa rufuwa, bayan komai ya lafa ne. Aka ba su salama Haneefa, sai gida. Wanda zuwa wannan lokaci, tuni Muhseen ya sami labarin haihuwar. Aje komai yayi, ya kamo hanyar Jigawa, cike da jin dadi da farin-ciki, ai ko bai shigo ba, sai sha biyu da kwata na dare, tun zuwansa, yana rungume da yarsa yana yi mata addu'o'i. ya dubi Haneefa. Wacce ciwon ciki ya matsa mata. Ya shiga yi mata sannu, tana amsawa da kyar. Tausayinta ya kama shi. Mata kam! Suna aiki, haihuwa ba karamin al'amari ba ne. A ganin Muhseen, ai dole maza su ji tausayin mata, su kuma darajasu, shi yasa yake mamakin wasu mazan da ba su maida mata a bakin komai ba, wanda, kuma kuskure ne babba. Haka gidan Sheik Sadisu yayi ta daukar jama'a 'yan barka, gidan bai sarara ba har sai da aka yi suna. Yarinya ta ci sunan Hajiya Goggo, wato Maimunatu.