Page 98
Ranar sunan kam! An tara jama'a. Me-jego kuma ta sami kayan arziki, domin hatta Sheik Sadisu, ba-karamin kaya ya hada mata ba, balle fa uban gayyar wato, Muhseen. Yayi mata kaya, ita da Maimunatu na garari, don ma bai da wadatattun kudi a lokacin. Amma Hameefa ai ta sami kaya, babu adadi. Mako daya cif! Da suna Muhseen ya koma Delta, ya bar Haneefa a dakin Hajiya Goggo, anan za ta yi zaman jegon, saboda ta sami kulawa, ita da jaririyar. Rayuwa kenan! Komai lokaci ne. Yau Muhseen ne ya mallaki 'yar kansa. Sheik Sadisu me kwadayin kada ya mutu, bai ga auransa ba, yau ga shi yana raye har yar Muhseen ya gani. Tsoho kenan, me ran karfe. Ruyuwar Muhseen Usman Jigawa ta ci-gaba a garin Delta, cikin natsuwar zuciya da aikin sadaukar da kai, har zuwa lokacin da aka ma ma fi yawancinsu canjin wajen aiki, wanda canjin wajen aikin ya ritsa da Muhseen da Umar, kuma wani abin ban sha'awa, duk waje daya aka kara hadasu, wato Legas. Cikin kankanin lokaci aka gama, duk abinda yakamata, kowa ya koma inda aka tura shi, wadanda kuma aka barsu a Delta, suka cigaba da tafiyar da rayuwar aikinsu anan. Muhseen ya sami kansa cikin canjin yanayi, a bisa dawowarsa Legas, inda bai taba rayuwa ba, yawan hayaniya da yawan cinkoso. Yana daya daga cikin abinda yasa Muhseen yake ganin tamkar ba zai ji dadi rayuwa, a garin ba, domin dai shi mutum ne me bukatar shiru da rashin son damu hayaniya ko takura, duk da gidajensu inda ma'aikatansu suke yana da saukin hayaniya, gidansu daya da Umar. Cikin kankanin lokaci Muhseen ya fahimci sakaci da rashin riko da addini da ma fi yawancin ma'aikatan musulmai da ke wajen suke yi, babu ruwansu, banda shaye-shaye da neman mata, ba abinda suke yi. Tamkar ba 'Ya'yan musulmai ba. Muhseen ya samu kansa cikin bakin ciki da tashin hankali, a dalilin hakan, ya sami wani tsaftataccen fili dake harabar gidajen nasu, ya zagaye shi da duwatsu, ya kuma fitar da kudi ya sayo tabarmi, ya shimfida, da zaran lokacin sallah yayi, ya kan fito ya kira sallah, tun yana yin sallar daga shi, sai Umar, har massalacin ya fara cika da mutane.