Page 99
Daga nan wadanda ba musulmi ba a wajen suka fara korafin gaskiya ana takura musu. Amma babu yadda za su yi, domin Muhseen tsayayyan namiji ne, mara tsoro, don haka ko darr! Bai taba yi ba, akan kudirinsa na janyo hankalin dubban musulman dake wajen, wadanda suka shagala da rayuwar duniya. Cikin kankanin lokaci Muhseen yayi fice aka san shi, ya kuma sami girmamawa da mutuntawa daga jama' ar wajen. Yau lahadi, haka nan Muhseen ya sami kansa da sha'awar zagaya garin Legas, domin tunda ya zo Legas, bai taba cire rana yayi yawo a cikinta, ya fahimci yadda take ba, bai fita tare da Umar ba, a dalilin ciwon kan da yake yi. Shi kansa Muhseen din, sai wajen karfe biyar, sannan ya fita, don da kamar ya fasa fitar. Saboda rashin Umar, amma haka nan ya ji zuciyarsa na azalzalarsa da dole sai ya fita, yana sanye da riga da wando na wani farin yadi, cikin motarsa wa'azin Malam Kabir Gombe ne ke tashi, wanda yayi akan aure a garin ruwan dorawa, jihar Zamfara. Wanda yayi a bikin Atiku da matarsa Shamsiyya. Muhseen ya maida hankalinsa kan sauraron kaset din, hakika da jama'a sun san falala da albarkar dake cikin yin wa'azi a bikin aure. Da duk an daina wanna fate-faten na banza da wofi, wadanda suke gurbata auratayyar. Tafe yake yana wannan tunanin, ya shiga nan, ya bulle nan, har ya fado wani titi me dan karancin cinkuso, ya daga kansa yana kallon gefan hanyar mata ne reras! Sun yi layi a bakin titin, gaba dayansu suna cikin banzar shiga, wanda bai taimaka wajen rufe ainihin jikinsu ba, wani abin takaici, ma fi yawancinsu musulmai ne. Duk da dai mawuyaci ne mutum ya iya fadin haka kai tsaye. Wannan wane irin rayuwa ce? Abinda Muhseen ke fada kenan a zuciyarsa, wadannan mata babu tantama ko shakkar cewa karuwaine. Domin da yawa maza, suna tsayawa su yi ciniki, da zaran cininkin ya fada, ya kan dauketa a motarsa, su tafi. Bakin cikin Muhseen ya karu. Wadannan mata gaba dayansu dakin miji, shi ne ya fi dacewa da su, domin dai wanna rayuwar, rayuwa ce ta ban tausayi, mara dadi, Muhseen ya cigaba da kallon fuskokinsu.cike da tausayawa