KALUBALE BOOK 1

Page 100

by @yargidanimam

A hankali yake jan motar tasa, idanun Muhseen cak! Suka tsaya akan idanun wata kyakkyawar dirrariyar yarinya, tana sanye cikin riga da siket matsattsu, domin dai hatta numfashi, wahalar fita yake mata. Kai! Amma Allah yayi halittar kyau a fuskarta. Gaba daya sal Muhseen ya sami kansa cikin gigicewa da dimaucewa a sanadiyar hada ido da wannan kyakkyawar yarinyar, domin dai rin idanunta ba za su taba bace ma tunaninsa ba, idanun yarinyar ba su da maraba ko banbanci da fitinanun idamun da yake gani a cikin mafarkinsa, irinsu daya, hatta gashin saman idonta, irin na cikin mafarkinsa ne, babu abinda ya raba su. Nan da nan Muhseen ya ji tsigar jikinsa na tashi, gaba daya kafafunsa san dauki rawa, cikin zafin nama ya shiga neman wajen (Parking), yana tsaida motar, ya fito da saurin gaske, ya nufi wajen yammatan , amma wani abin takaicin da tashin hankali, ga Muhseen, shine yana isa wajen yarinyar, na shiga wata katuwar motar (Jeep) ba-ka wuluk! Tana shiga, tamkar walkiya. Mamallakin motar, ya ja-ta, suka bace ma idanun dake wajen . Ta Gaban Muhseen motar ta wuce, haka ya tsaya galala yana kallon motar, har ta bace ma ganinsa. Ya rintse idonsa, haushi yana kara kamashi, a hankali ya bude idonsa, ya juya yana kallon sauran kalilan din 'yammatan dake wajen, ya rasa abin dake masa dadi. A hankali ya juya zuwa waje motarsa ya fi minti shida zaune a cikin motar, ya rasa abinda yake tunani, daga bisani ya tada motarsa, bai yi tunanin ci-gaba da shiga cikin garin Legas ba. Ya juya zuwa gida cikin matsanancin tashin hankali da zafin zuciya, yana shiga falo, ya fada kan kujera yana maida numfashi, sai ka ce wanda aka biyo da gudu. Umar ya dago yana dubansa yace "Ka gaji kenan, an sha yawo, ya ka ga cikin garin Legas din? Haka ya ci-gaba da jero masa wadanan tambayoyin amma Muhseen ya kasa cewa uffan Umar yasa masa ido cikin kankanin lokaci ya fahimci Muhseen yana cikin damuwa ya sauko daga kan kujera ya dawo kusa da shi ya dafa shi firgigit yayi yana dubansa da ido abude Umar yace "Muhseen yaya dai? Me ya faru da kai ne?" Muhseen ya saki ajiyar zuciya a sanyaye yace "Umar na ganta yau, na ganta", Cikin rashin fahimta Umar yace "Wace ce? Wa ka gani?"

Ku dakace ni

Daga taskar

Yar gidan imam KALUBALE BOOK 1 HABIBA ABUBAKAR IMAM (MRS ALIYU MAYERE)

Bismillahir Rahma Nirrahim