KALUBALE BOOK 1

Page 101

by @yargidanimam

Muhseen ya tashi ya zauna yana kallonsa cikin matukar gigita yace 'Dama na san ba aljana bace, kuma ba shaidan bane, yau na ganta, idanun da nake gani a cikin mafarkina, wanda ban taba ganin wata 'ya mace da irin su ba. Yau naga macen da ta mallaki irin idanun Umar. Kamar yadda idanunta suke da kyau, haka fuskarta da jikinta suke da matukar Kyau, ban taba ganin mace me kyawunta ba". Umar ya gyara zama cike da mamaki yace "Kada dai har yanzu ace kana nan akan ba-kanka, da Allah ka bar maganar nan". "Ya za ka ce na bar maganar? Bayan ina gaya maka yau na ganta, kuma Umar ina ganinta sai na ji wani matsanancin so da kaunarta ya kamani, kwatankwacin irin son da nake ma ta a mafakina, kai har ma ya fi". Umar ya fahimci dai da gaske Muhseen yake, don haka ya matso kusa da shi yace 'A ina ka ganta Muhseen"? Yayi dan jim! Alamar jin haushi da jimamin halin da ya sameta a ciki, a sanyaye ya dubi Umar yace "A bakin titi na ganta Umar, kuma ga dukkan alamu Karuwa ce." Umar yayi gaggawar hadiye yawun da yake neman ya shake shi, saboda firgita da maganar Muhseen, yace 'Karuwa Muhseen? “ Ya gyada kai. "Kwarai da gaske Umar, karuwa ce'. Umar yayi dif! Bai kara yin magana ba, tsawon wani lokaci, sannan Muhseen yace "Umar ba-ka ce komai ba, don Allah ka yi Magana, ka ce wani abu", Umar ya numfasa yace "Me zan ce? Abin me girma ne Muhseen, ka fita daga batun wannan mafarkin naka, ina kai, ina karuwa? Ba-ka da hankali ne, za ka fada son karuwa da mutuncinka da komai? Wannan ba maganar yi bace". Muhseen ya kura masa raunannun idanunsa masu cike da tashin hankali yace "Umar tunda nake, ban san so ba, sai akan wadannan idanun, yanzu kuma da Allah ya hadani da wannan yarinyar, sai na sami kaina da yi mata wani irin matsanancin so. Umar ba-ka san yadda nake ji akan yarinya nan ba, ina matukar sonta Umar, ina sonta, na rantse ko da a mugun halin da yafi karuwanci na ganta sai na so ta, kuma sai yay nagane ma’anar mafarkin da nake yi akan tana cikin katon rami tana miko hannu na cirota , tabbas karuwancin da take yi shine katon ramin da nake ganinta ciki , don haka hannu da take miko min kuma zan kama zan cireta a cikin wannan masifar da take ciki,don Allah umar Ka taimaka min". Umar ya dube shi cikin daurewar kai yace "Na taimaka maka ka ci-gaba da son karuwa? Wannan wace irin tabewa ce Muhseen da kimarka da darajarka ka fada son karuwa, wacce ba-