KALUBALE BOOK 1

Page 102

by @yargidanimam

ka san inda take ba, ba-ka san komai nata ba. Anya abin naka na lafiya ne?" Muhseen yace "Rashin sanin inda taken a yanzu shine kadai damuwata, amma zan nemeta, duk inda take a garin Legas, sai na kwakulota." "Lalle aiki ya sameka. Allah ya kyauta".cewar umar cikin rashin amincewa da halin da yake son jefa kansa. Bai kuma yi masa Magana ba, shi ma Muhseen bai kara cewa uffan ba, ya koma ya kwanta akan kujera ya maida idanunsa ya rufe. Surar yarinyar kawai yake gani a cikin duhun. A gaskiya Allah yayi halitta, fuskarta, fuska ce me cike da kamala, da shi yasa yake. mamakin ganinta a cikin irin wannan muguwar rayuwa ta karuwanci, A zahiri, duk yadda zai yi, yayi alkawarin sai yayi, domin ganin ya lalubo inda yarinyar take, duk da dai ya san mawuyaci ne ya iya nemota a babban gari kamar Legas. Sai dai duk da haka, ya kudiri aniyar nemota, ya kuma sha alwashin rabata da muguwar sana'arta ta karuwanci. So bala'i ne! Domin dai a wannan daran Muhseen bai iya runtsawa ba. Karfe uku ya tashi ya dauro alwalarsa kamar yadda ya saba, ya shiga gabatar da sallar nafila, sai dai yau addu'ar tasa ta fi karfi akan Allah ya hada shi da yarinyar daya gani yau ne. Sai kuma fatan shiriya da yayi mata.