KALUBALE BOOK 1

Page 103

by @yargidanimam

Washegari sukuku ya tashi tamkar bai da laflya, yayi kokarin kammalawa da komai da wuri, daga nan ya fice ba tare daya nemi rakiyar Umar ba, domin ya fahimcl Umar bai gasgata abinda ya fada masa ba, ya dauki maganar tasa tamkar wasan yara. Muhseen na fita, kai tsaye titin daya ga yarinyar ya nufa Yauma wajen cike yake da mata, ya tsayar da motarsa, ya fito ya taka zuwa wajensu, yana kallonsu daya bayan daya. Amma abin haushi gaba daya ba fuskar yarinyar. Kusa da wata dogurwar yarinya ya tsaya yana kallonta, sannan yace"Don Allah ina bukatar yin magana dake? “ Ta juyo tana kallonsa, ganin Yadda ya hadù, yana da kyau abin alfaharin duk wata ya mace ne, nan da nan ta shiga murmushi tana gyara shegiyar rigar jikinta, wanda duk rabin kirjinta a waje yake. A zatonta Muhseen tayawa ya zo yi. Can gefe ya koma, ta biyo shi ta tsaya gabansa tana karairaya. Muhseen ya dan dubeta yace "Ya sunanki? Tayi murmushi tace "Sunana Ummancy", "Ainihin sunanki nake son na ji". Ta dan tsare shi da ido, sannan tace "Sunana Sakina'. Ya gyada kansa yace "Tambaya nake son na yi miki" "'Allah yasa na sani". Ta fada tana lumshe ido, yace 'Wata yarinya nake tambaya." Daga nan ya shiga zayyana mata kamanninta. Sai daya gama tsaf! Sannan Ummancy tayi jim! Tace "Tana yawan zuwan nan, amma yau ban san abinda ya hanata zuwa ba." Muhseen yace "Kin san sunanta? " ta dan yi jim alamar tunani, sannan tace “Tee-Baby na ji ana kiranta". Muhseen ya maimaita a hankali "Tee-baby". Ummancy tace "Shi kenan, zan koma bakin kasuwancina." Muhseen yayi gaggawar cewa "Kada ki damu, ba kudi kika fito nema ba? Zan ba ki ko nawa ki ke so, amma ina bukatar taimakonki." Ummancy ta ji batun kudi, nan da nan ta gyara tsayuwarta tace "Wane taimako kake nema, kuma Malam?” Muhseen yace 'Ina son ki nuna min gidan da take? Ummancy ta girgiza kai tace "Nan fa daya, domin dai ban san gidan da take ba, mu kan dai hadu anan, ka zo, na zo. Wata rana mu yi ma