KALUBALE BOOK 1

Page 105

by @yargidanimam

dakata tana kalionsa tace 'Sa gobe kenan". Yace "Don Allah ki jirani a inda na daukoki goben." Ta girgiza kai "Ban ga amfanin fitata ba goben, tunda ko na fita, ba barina za ka yi na yi (Business) dina ba, don haka ka sameni a gidan nan, ga lambar wayata, da ka zo ka kirani". Ya fito da wayarsa, ta gaya masa lambar. Ya zuba a ta shi wayar. Ya dago yana kallonta yace "Ki na da kirki Sakina. Allah ya saka miki da alheri". Ummancy tayi murmushi tace "Ba ni da wani kirki, ni kaina, Ina mamakin yadda nake da shaa'awar taimaka maka neman Tee-baby, amma dai na san ka na burgeni." Ta karasa fita daga motar. Muhseen na yi mata godiya, bai bar kofar gidan ba, har sai da ya ga shigarta gida, sannan ya tada motarsa ya tafi, zuciyarsa cushe da bakin ciki da radadin rashin ganin Tee-baby, gaba daya rigarsa jike take da zufa, a gajiye yake lilis! Shi kansa ya manta rabonsa da sa wani abu a cikin cikinsa, haka ya isa gida, yana shiga falon, bai damu da ganin Umar zaune jugum ba, ya fada kan kujera, yana aje numfashin jigata da wahala. Tsawon lokaci, babu wanda yayi ma wani magana tsakanin Muhseen da Umar har zuwa lokacin da agogon falon ya buga karte goma sha daya na dare, wanda yayi dai-dai da lokacin da cikin Muhseen yake kururuwa. Umar ya kauda shirun da cewa. "Muhseen ina ka shiga? Ina ka je, don Allah har tsawon wanna lokacin, babu tunanin zan iya shiga damuwa, tunda ba-ka taba yi min irin wannan ba, ba-ka taba fita ka dau lokaci ba-ka dawo ba, ina ka je? Muhseen ya dago yana kallon Umar. Shi ma kallon nasa yake, ya dan nisa yace "Ka yi hakuri, na fita nemanta ne?" a gaggauce yace "Anya Muhseen kana cikin hankalinka kuwa?” A hankali yace "Ina cikin hankalina Umar, yakamata kuma ka tsaida hankalinka ka fahimceni, ka kuma gasgata maganata, sunanta Tee-baby, ita ce ta mallaki soyayyata, ta kuma mallaki idanun da nake kwadayin gani a zahiri". Yayi shiru yana kallon Umar, wanda ya kasa cewa uffan, illa ido daya sa masa, ganin hakan, yasa ya ci-gaba da cewa "Na je