Page 106
gidajen karuwai sama da tara, ina nemanta ni da wata karuwa Ummancy, da ta taimaka min, ta rakani gidajen karuwan. Amma ba mu yi nasarar ganinta ba, ko samun wanda ya santa ko ya san ainihin gidan da take. Amma tun. fitata ina can billayin nemanta" Umar ya saki salati yacie "Muhseen wane irin KALUBALE! Ne ya sameka? Tee-baby? Kana cikin hankalinka kuwa? Yau ni na shiga uku! Jama'a na nan na jiranka ka ja musu limanci, ka barsu cikin tunanin inda kake, ashe ka nan can gidajen karuwai. Wa'iyazubillah! Muhseen idan barci kake, to Wallahi ka farka, babu yadda za'ayi ka yi soyayya da karuwa, ko ka manta da tamabarinka na Malami, dan Malaman ne, wanda kake nema ma kanka ingatacciyar rayuwa, wace ce Tee-baby, don Allah?”. Muhseen yayi gaggawar tashi ya zauna, yace yana kalion Umar "Ka daina wannan maganar, ina cikin hankalina sarai! Kuma na yi alkawarin sai na mallaki Tee-baby, domin na sha alwashin sai na fitar da ita daga muguwar rayuwar da take ciki, don ina dan Malamai, sai na na kasa yin hulda da karuwa? Kada fa ka manta karuwa ce, ba wai kafira ba, akwai alaka me karfi tsakanin musulmi da dan-uwansa musulmi, meye aibu? Don zan fitar da ita daga karuwanci, na aureta, ina da lada me yawa, domin tamkar jihadi na yi". Umar ya numfasa yace "Muhseen, me ya haukataka ne? Don Allah ka bar maganar nan, idan kai kana tunanin za ka aureta, ita ka na tunanin auren ne a gabanta? Kai ba ma wannan ba, shin ka na da yakinin za ka kara haduwa da ita? Muhseen yace "Kwarai kuwa, ina da tabbacin zan hadu da ita, tunda Allah ya kallafa min kaunarta, na san zai hadani da ita. Ni dai fatana shine ka goya min baya, ka taimaka min neman Tee-baby, domin ina cikin wani babban KALUBALE." Umar ya gyada kai cike da damuwa yace 'Shi kenan. Allah ya kyauta, ya tsare.” Muhseen yace. "Ameen." Gami da komawa ya kwanta. Umar ya tsare shi da ido yana cike da mamaki da tausayin Muhseeen akan jarabtar da Allah ya dora masa, idonsa na rufe yace "Umar babu abinci a gidan nan? Rabona da abinci har na manta." Umar ya girgiza kai yace "Allah ya kyauta, babu amma bari na je na nemo maka." Ya yunkura