KALUBALE BOOK 1

Page 107

by @yargidanimam

ya tashi, ya fice. Cikin kankanin lokaci ya dawo dauke da tuwon shinkafa, ya aje a gabansa. Sai da Muhseen ya ci, ya koshi, yayi hamdala, sannan ya tashi yayi alwala. Urnar yau na ganin abinda bai taba gani ba. Muhseen yana hada salloli, yayi tsuru har ya kammala, yayi addu'a, ya shafa., sannan ya juyo ga Umar, idon da ya ga ya sa masa, yasa yace "Yaya ne Umar?" Ya dan numfasa yace "Ka na ganin hulda da haduwarka da Tee-baby Alheri ne? Muhseen ya dan lumshe ido, ya bude yace "Me yasa ka yi min wannan tambayar?” Umar yace "Saboda tsawon shekarun da na yi tare da kai, komai cudewar aiki, ban taba ganin ka hada salloli ba, sai yau da ka hadu da Tee-baby, shi yasa na ke ganin haduwvarka da Tee-baby, ba alheri bane". Muhseen ya rintse Idanunsa , ba shi da wani baki da zai fahimtar da Umar, domin dai shi kansa ya san bai kyauta ba, yayi kuma sake... Kukan da wayarsa ta shiga yi, yasa ya bude idonsa, ya dauko wayar. Ganin sunan Haneefa yasa ya rarimi wayar da sauri, domiin dai rabonsa da jinta, tun jiya. Abinda bai taba yi ba, tun bayain haihuwar Iman, wato Maimunatu, ka'ida ne kullum ya kira waya, ya ji lafiyarrta da ta 'yarsa Iman, wacce yake matsanancin kauna. "'Haneefa." Abinda ya fara fada kenan. Tayi murmushi "Babban Yaya lafiya? Aka samu a kwandon shara, jiya ban ji ka ba, yau ma ban jj ka ba, yaya dai?" Muhseen ya kudunune idanunsa, baya son yayi mata karya, amma ba yadda ya iya. Yace "Ni ma ba haka na so ba Haneefa. Aiki ne ya cude min, babu sukuni, dama yanzu nake shirin nemanki, na ji lafiyarki da ta Iman. Yaya babu wata damunwa ko?” Ta girgiza kai "Ba wata damuwa, sai dai jiya Iman garin rarrafe ta fadi goshinta yayi kulu". Muhseen ya zabura ya tashi, ya haye kujera "Ta yi kuka, sosai ko?” Tayi dariya, tace "Can na mikata wajen Hajiya tayi kukanta, ta more." Muhseen yayi tsaki yace "Sakacinki ne. Ya za'ayi kin san yarinya na rarrafe, amma sai ki tafi, ki barta ita kadai? “ Haneefa tace "Wa ya gaya maka ita kadai ce? Tare fa muke", "To gaskiya ki dinga kulawa, kuma ki kaita asibiti a dubata."