KALUBALE BOOK 1

Page 108

by @yargidanimam

Haneefa tayi dariya sosai tace "Kai Babban Yaya, kulu ne fa kawai tayi, ya kuma baje. Da akwai wata damuwa, ai da tuni na kaita asibitin", "To shi kenan, a dinga dai kulawa". Ya fada ya na aje numfashi, Daga nan suka ci-gaba da 'yar hirarsu. Umar idonsa na kan Muhseen, har suka yi sallama, ya aje wayar. Idon da Umar yasa ma sa ne, yasa ya tashi ya shige daki, yayi kwanciyarsa, domin ya ji dadin ci gaba da tunanin Tee-baby. Washegari kuwa Umar ya na ganin Muhseen yayi shirinsa cikin riga da wando na shadda, yayi matukar kyau, kwarjininsa ya kara fita. "Umar na fita." Abinda yace kenan, a lokacin da yake kokarin wucewa ta gabansa, shi ma Umar din a gajarce yace "Ka na bukatar rakiyata? “ Cikin jin dadin maganarsa. Muhseen ya juyo yana murmushi sosai, yace "Neman Tee- baby zan fita fa." Umar ya yunkura ya tashi yace "Na sani." Muhseen yace "Na gode, mu je". Ya fita Umar ya bi-shi a baya, zuciyarsa cike da sake-sake. Cikin kankanin lokaci, sai ga su a unguwar Ajagule, lalle kam! Sai Ajagulen. Abinda Umar ya fada kenan, a lokacin da Muhseen ya tsaida motarsa a gaban gidansu Ummancy. Shi kansa Muhseen sai yanzu ya kara ganin lalacewa da kazantar unguwar. Musamman kofar gidansu Ummacy da wata lafiyayyar kwata tayi male-male, sai wari, a hanzarce ya kira Ummancy a waya. Bugu daya, ta dauka, ta kuma tabbatar masa ga ta nan fitowa, tamkar ta kosa ta fita. Domin bai wuce minti uku da aje wayar ba, ta fito daga cikin gídan. Yau dai shigarta da dama, domin wata doguwar riga ta sa, ta atamfa wacce aka matse kirjinta, babu ko da karamin gyale, sai jaka da ta riko katuwa, tamkar me shirin zuba kudin duniya a ciki, "Ranka ya dade, ka so ka taki sisi". Cewarta tana kokarin bude bayan motar ta shiga. Muhseen yayi murmushi yace "Ayi min afuwa, ni ma na so fitowa da wuri". Ta maida kofar ta rufe, ya ja suka fara tafiya, tana fadin "Ni ma ba cewa na yi ka zo a makare ba, bako na yi, ya bukaci na yi masa rakiya, shine na gaya masa akwai inda zan je.”