Page 109
Muhseen ya kara murmusawa yace. "To nace ki na da kirki, kin ce ba ki da wani kirki, in ban da ki na da kirki, ai da kin mantani da alkawarin mu". Tayi dan murmushi tace "Malam, ai ni duk barikina, ban yarda da saba alkawari ba". "Ki kirani Muhseen, kuma cika alkawari dabi'ace me kyau, wacce Allah ke mutunta duk me cika shi. Cika aikawari kuma yana kara darajar mutum, don haka ki ci gaba da rike alkawari kamar yadda nake yi miki addu'ar fatan shiriya, ki tuba ki bar wanna gurbatacciyar sanar'a". Ummancy tayi ajiyar zuciya tace "To ba zance ba amin ba, amen. Abokinka ne wannan?" Muhseen ya amsa 'Eh, abokina ne, tare muke". Umar ya dubeta yace "Ina gajiya? Ta amsa da sauri "Ba gajiya, sannu". Umar bai kara magana ba. Muhseen yace "Ina muka yi ne Sakina? Ina ta ba mota wuta". Tayi murmushi. Daga nan ta nuna masa hanyar da zai bi, sannu a hankali suka yi ta tafiya. Su shiga nan. Su shiga can. Sau tari wani lokacin Ummancy ce ke shiga gidan karuwan ta bincika masa Tee-baby. Sai da suka shiga gidan karuwai shida, amma babu koda me kama da Tee-baby, hakurin Umar ya gaza. Ya dubi Muhseen yace "Idan kai ba-ka jin yunwa, dan ajeni, na sami abinda zan ci, don ni yunwa nake ji". Ba tare da Muhseen yace komai ba, ya karkata akalar motarsa zuwa wani (Restaurant), hankalinsa a tashe yake, don haka sam bai iya cin komai, bayan kallon Ummancy da Umar suna dankara loma lakadan! Hankalinsu kwance, yayi sha'awar ina ma shine hankalinsa ke kwance haka. Haduwarsa da Tee-baby, ya haddasa ma rayuwarsa canjawa, ya fada wani hali na tunani da damuwa,. Sai juya cokalin hannunsa kawai yake a cikin jolof din shinkarfar dake gabansa. Har su Umar suka kammala ci, kamar daga sama ya ji Ummancy tayi masa tambayar "Muhseen dan Allah ya kake da Tee-baby, meye dangantarkaku? “ Shi kansa Umar ido yasa ma Muhseen, ya ji irin amsar da zai bata. Ya dago yasa ma Ummancy ido, sannan yace "Kin san so?"