KALUBALE BOOK 1

Page 110

by @yargidanimam

Ummancy ta rausayar da kai, idanunta duk suka canja, tace a sanyaye "Na san so! Domin so shine sanadiyyar fadawata wannan halin na karuwanci". Muhseen ya runtse idanunsa, tausayin Ummancy ya kama shi, ya bude ido yana kallonta. Yace "Lallai kin san so! To so shine dangantakar dake tsakanina da Tee-baby, ina tsananin kaunarta, tun daga ranar dana fara ganin irin idanunta a cikin mafarkina da Allah ya hadani da irin idon a zahiri. Sai ya zama mailakar Tee-baby ne. Na ga mata da yawa a duniya, amma ban taba ganin me irin idanun Tee-baby ba, don haka na fada kogin kaunarta, abinda ban taba kwatantawa akan wata 'ya mace ba". Ummancy tasa masa ido, tana jin tausayinsa kwarai da gaske, domin dai ta san so, ta san kuma zafin so, ta kuma san idan ba so din ba, babu abinda mutum kamar Muhseen, wanda take ganin mutunci da kamala a tare da shi, zai yi da mace kamar Tee-baby, karuwa! A hankali Ummancy tace "Na fahimci yadda kake ji a game da Tee-baby, saboda haka zan taimaka maka nemanta, za kuma mu ganta matukar tana cikin garin Legas, ka kwantar da hankalinka." Muhseen yayi matukar jin dadin maganar Ummancy, yayi mata godiya sosai. Umar ya nisa gami da zuba tagumi, ya rasa irin wannan al'amarin na kaddara da ta fado ma Muhseen. Daga bisani Ummancy ta dube shi tace "Ka bar komai a hannuna, kada ka kara damun kanka, ka bar uzirinka, ka fito nemanta, ni zan nemar maka ita, tunda kuma ina da lambarka. Da zaran na ganta, zan kiraka, don na sanar .da kai". Ba Muhseen ba, hatta Umar ya ji dadin wannan mutunci da karamci na Ummancy, hakan kuma ya kara tabbatar musu da cewa duk lalacewar mutum, ba zai rasa wani kyakkyawan hali ba a cikin halayyarsa ba. Ummancy kam! Ta gama masa komai, ba kuma zai taba mantawa da taimakonta gare shi ba. Don duk wanda zai hada shi da Tee-baby, bai da kamarsa so kenan! Daga (Restaurant) din, kai tsaye ajagule suka koma. Suka aje Ummancy a kofar gidanta, bayan Muhseen ya mika mata Naira dubu ashirin. Ta amsa cike da mamaki tayi masa godiya, sannan ta shige gída cikin farin-ciki. Ya ja motar suka tafi, har suka kusa gida,

Ku dakace ni

Daga taskar

Yar gidan imam KALUBALE BOOK 1 HABIBA ABUBAKAR IMAM (MRS ALIYU MAYERE)

Bismillahir Rahma Nirrahim